Tsohon sanatan Zamfara a majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Marafa ya lashi takobin ganin sai Mala Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC ko yaki ko yaso.
Marafa ya ce babu inda dokar kasa ko kuma na jam’iyya ta ba wanda ke da mukamin gwamna ya rike kujerar siyasa kuma ” A dalilin haka tabbas zan garzaya kotu domin a fassara min hujjar da ya sa Mala Buni ke rike da kujerar shugaban jam’iyyar APC duk da yana gwamnan jiha.
” Ba za ta sabu ba, dole sai Mala Buni ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar APC ko ya ki ko ya so. Zan garzaya kotu domin a tabbatar masa cewa karya doka ce zaman sa shugaban jam’iyya bayan kuma yana rike da mukamin gwamnan jiha.
“Wane ne ya zabi Buni da kwamitinsa? A wani babban taro ko majalisa? Ni dinnan da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu ‘yan APC muka yi ruwa mu kai tsaki har Buni ya zama sakataren jam’iyyar a shekarun baya.
” Sannan kuma zamu bukaci lallai menene doka tace game da duka abubuwan da ya gudanar a tsawon lokacin da yake shugabancin jam’iyyar har zuwa yanzu.
” A cire wannan mutumin daga shugabancin jam’iyyar APC tun da wuri kafin ya yi ragaraga da ita, na fito aikin ceto ne.