Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana cewa ayyukan gyaran titinan Najeriya a shekarar 2022 ya na buƙatar naira tiriliyan 1.3, maimakon cikin-cokali naira biliyan 450 da aka ware wa ma’aikatar sa a kasafin 2022.
Da ya ke bayanin kare kasafin 2022 na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya, Fashola ya sake bijiro da wata matsalar cewa a yanzu haka ‘yan kwangila na bin Gwamnatin Tarayya bashin naira biliyan 450, duk na aikin titina da su ka yi, amma ba a biya su ba.
“Naira biliyan 282.6 kacal aka ware za a kashe wajen ayyukan titina a shekarar 2022. Wannan kuɗi kuma sun yi kaɗan matuƙa.
“Shi ya sa muka yanke shawarar za mu daina gina sabbin titina, amma za mu bada fifikon ayyukan gyaran titinan da aka fara da kuma titina masu muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya. Wato kamar titunan da suka doshi tashoshin jiragen ruwa da kuma yankunan da ake hada-hadar ayyukan noma.”
Yayin da Fashola ya koma bibiyar kasafin 2021 da ya wuce kuwa, ya bayyana wa kwamiti cewa an ware wa manyan ayyuka da gidaje naira biliyan 347. Amma har zuwa yau kusan ƙarshen shekarar 2021 ɗin, naira biliyan 182.9 a cikin kuɗin kaɗai aka ba ma’aikatar sa, domin yin manyan ayyukan.
Don haka ya ce ma’aikatar sa ta daina aikin gina sabbin titina, saboda ƙarancin kuɗi. Maimakon haka, za ta fi maida hankali wajen kammala waɗanda aka fara.
A ƙarshe ya shawarci ‘yan Majalisar Tarayya su karkata ayyukan mazaɓun da ake ba su wajen gina titina da kuɗaɗen a yankunan su.
Shugaban kwamiti Abubakar Kabir daga Jihar Kano, ya ce lallai akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta fito da wasu hanyoyin da za ta samu kuɗaɗen ayyukan gina titina.
Discussion about this post