Ministan Tsaro Bashir Magashi, ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta sun haddasa barazanar ƙarancin abinci a ƙasar nan, abin da ya kira “wata sabuwar barazanar da ta kai cikin ƙasa.”
Magashi wanda Manjo Janar mai ritaya ne, ya yi wannan bayani a wurin taron sanin makamar aikin da Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji (DIA) ta shirya wa Mashawartan Fannin Tsaro da kuma wakilan Hukumar Tsaro da ke aiki ofisoshin Jakadun Najeriya a Waje.
An shirya taron ne a ranar Litinin a Abuja.
Magashi ya ce hare-haren da Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kaiwa a yankin Arewa maso Gabas da kuma hare-haren da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ɓarayij shanu da kuma rikicin makiyaya da manoma a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sun zama babbar barazana ga tsaron Najeriya.
Magashi ya ce su kuma wasu ɗaiɗaikun jihohin Kudu maso Kudu na fama da ɓarayi masu fasa bututun mai, ‘yan tada zaune tsaye, masu sumogal a ruwa, yayin da yankin Kudu maso Gabas kuma ke fama da masu ƙoƙarin ɓallewa daga Najeriya, wato tsagerun IPOB.
Ya ce shi ma yankin Kudu maso Yamma na fama da masu ra’ayin kafa ƙasar Yarabawa masu ƙabila ɗaya, kuma a can ma ana fama da tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma.
“Babban abin takaicin, wannan matsalar rashin tsaro ba ga tsaro kaɗai ta ke ƙalubale ba, har ma ga abinci ta zama babbar barazana.
“Musamman ana fuskantar ƙarancin abinci da kuma yawaitar hauhawar farashin kayan abincin a faɗin sassan ƙasar nan.
“Saboda haka abu ne mai muhimmanci dukkan ɓangarorin tsaron ƙasar nan su haɗa hannu wuri ɗaya domin samar da tsaron da zai kakkaɓe waɗannan barazana da sassan ƙasar nan ke fuskanta.”
Yin hakan a cewar Magashi zai sake zaburar da jama’a wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da yanayin da masu zuba jari daga waje za su bijiro ga Najeriya.
Ya ce jami’an tsaro sun yi rawar gani matuƙa, inda nasarorin da suke samu ne ta kai ga har aka samu ‘yan ta’adda sama da 14,000 suka yi saranda.