A wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Gwarjo cikin Ƙaramar Hukumar Matazu, sun bindige mutum shida a ranar Juma’a da dare.
Mazauna yankin sun ce baya ga mutum shida da aka bindige, an ji wa mutum 9 raunuka a harin da ‘yan bindigar suka kai.
Wani mazaunin ƙauyen mai suna Musa Abdullahi, ya ce maharan sun isa garin wajen ƙarfe 9 na dare. Ya ce sai da suka shafe sa’o’i uku cur su na aika-aika a ƙauyen. Abdullahi ya ce sai da ‘yan bindiga su ka kai ƙarfe 1 na dare a Gwarjo.
“Wajen ƙarfe 9 na dare suka dira ƙauyen su na harbin kan-mai-tsautsayi. A haka su ka kashe mutum shida kuma suka ji wa mutum 9 raunuka.” Inji Abdullahi.
Ya ce an garzaya da waɗanda aka jikkata ɗin asibitin ƙashi na Amadi Kurfi da Babban Asibitin Katsina.
Waɗanda aka kashe ɗin sun haɗa da Abdu Bahillace, Ali Niga, Bello Yusuf, Ɗan Asabe Ubi, Sanin Ayya da Abdullahi Bello.
Abdullahi ya ce waɗanda ke da sauran kwana gaba sun haɗa da: Lawal Muhammad, Abubakar Sada, Muhammadu Sani, Isyaku Yahaya, Mu’awiyya Dogon Zikiri, Gambo Anas, Buhari Mamman Ibrahim Garba da Mamuda Yahaya.
Har Yau Ba Mu San Halin Da Wasu Ke Ciki Ba -Mazaunin Gwarjo
Wani mazaunin Gwarjo da ya ce a sakaya sunan sa, ya ce har yau ba a ji halin da wasu ke ciki ba, domin bayan an kai harin, an neme su ba san inda su ke ba.
Amma kuma ana kyautata zaton ba garkuwa da su aka yi ba, domin majiya ta ce ba su tafi da ko mutum ɗaya ba, sai dai sun ƙwaci babura a hannun jama’ar gari.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Katsina, Gambo Isa, amma ba a same shi ba.
An kai wannan hari kwana uku bayan an kashe mutum 12 a Batsari.