Mai rikon kwaryar kujeran Babban Alkali na jihar Adamawa Nathan Musa ya bayyana cewa a shekaran da ya gabata ma’aikatar shari’a ta saurari kararraki 100,000 sannan ta tara Naira miliyan 6.
Musa ya fadi haka ne a taron da ma’aikatar ta yi na shekarar 2021/2022 da aka yi ranar Litini a garin Yola.
Ya ce an yi rajistan kararrakin a kotunan yankin, manyan kotuna, kotun Majistare da kuma manyan kotuna.
“An sallami kararrakin 70 daga cikin kararrakin 100,000 din da kotunan suka saurara.
“Sannan ma’aikatar ta tara Naira miliyan 6 a cikin shekara daya wanda ta mika wa gwamnati.
“Ma’aikatar ta tara wadannan kudade a dalilin taran da take karba daga wajen mutane, kudin da ake karba na samu takardan haihuwa da sauran takardun da ake karba a kotu sannan da kudin da kotu take karba na shigar da kara.
Bayan haka Musa ya ce ma’aikatar na iya kokarinta wajen ganin ta sallami kararrakin cikin gajeran lokaci.
Ya ce a dalilin gyare-gyaren da aka yi ma’aikatar za ta dawo da biyan ma’aikatan da suka je hutu albashi da biyan kudin asibitin ma’aikata.
Musa ya kuma ce gine-ginen da kotunan na ma’aikatar na matukar bukatan gyara Wanda ya kamata a fara gyara su nan ba da dadewa ba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa gwamnan jihar Ahmadu Fintiri Wanda mataimakinsa Crather Seth ya wakilce shi a taron ya jinjina gyaran da Musa ya yi a ma’aikatar.
Seth ya Kuma Yaba inganta walwalan ma’aikata da Musa ya yi sannan ya ce gwamnati za ta ci gaba da mara wa ma’aikatar baya