Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Lura da Ɓangaren Shari’a, ya nemi gwamnati ta yi ƙwaƙkwaran bincike domin gano duk masu hannu wajen shirya makircin da jami’an tsaro suka kai Gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙolin Najeriya.
Mary Odili, wadda matar tsohon Gwamnan Ribas Peter Odili ce, ita ce ta biyu a jerin manyan alƙalan Najeriya na Kotun Ƙoli.
Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Tarayya, Luke Onofiok, ya ce ya zama tilas a gano dukkan masu hannu domin a hukunta su.
Ya ce irin wannan abin takaici da abin kunya da ya faru, ya na rage wa sashen shari’a kima, martaba da daraja ne a idon ‘yan Najeriya da idon duniya baki ɗaya.
Duk da cewa mijin ta Peter Odili ya na da matsala da EFCC, har ita EFCC ɗin ta sa Hukumar Shige-da-fice ta riƙe masa fasfo ɗin sa, amma EFCC ɗin ta ce babu hannun ta a farmakin da jami’an tsaro su ka kai gidan matar sa.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda aka shirya batarnaƙa a wata Kotun Majistare, har kotun ta bayar da sammacin umarnin binciken gidan Babbar Mai Shari’ar, bisa wasu bayanai da aka bai wa kotun a hagungunce.
Tuni dai bayan jami’an tsaro sun shafe sa’o’i a ƙofar gidan ta, wata kotu ta hanzarta soke wannan sammaci na binciken gidan.
Tuni shi ma MInistan Shari’a Abubakar Malami ya ce waɗansu tantagaryar ‘yan iska ne su ka tsara yadda jami’an tsaro su ka dirar wa Mai Shari’ar Kotun Ƙoli har gida -Ministan Shari’a Malami.
Ministan Harkokin Shari’a Abubakar Malami ya nesanta kan sa ko hannun ma’aikatar sa daga farmakin da jami’an ‘yan sanda su ka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli a Abuja.
Cikin wata sanarwa da Umar Gwandu wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami, ya bayyana cewa, “dirar mikiyar da jami’an tsaro su ka yi a gidan Mai Shari’a Mary Odili, akwai alamu na tantagaryar iskanci wajen ƙalla shirin.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Mary Odili ta ce ba ta yarda a shiga gidan ta ba sai da sammaci daga kotu, kuma gidan ta ba gidan mijin ta ba ne, Peter Odili, wanda ke da matsala da EFCC.
Malami ya bayyana cewa yadda aka yi asarƙakar bayanai a gaban kotu har aka bada umarnin tura jami’an tsaro a gidan, akwai tantagaryar iskanci a lamarin.