Sakamakon gwajin cutar Kwalara da hukumar NCDC ta fitar na mako na 41 ya nuna cewa an samu karin mutum 417 da suka kamu da cutar sannan mutum 21 sun mutu a jihohi bakwai a kasar nan.
Hukumar ta ce an samu karin ne tsakain ranar 11 zuwa 17 ga Oktoba 2021.
Daga watan Janairu zuwa ranar 17 ga Oktoba cutar ta yi ajalin mutum 3,283 sannan hukumar ta ce akwai mutum 93,362 da ke dauke da cutar a jihohi 36 da Abuja.
NCDC ta ce wannan karo cutar ta ci gaba da yaduwa a jihohin Arewa.
Jihohin da cutar ke ci gaba da yaduwa sun hada da Kaduna, Katsina, Kano, Yobe, Adamawa,Barno, Zamfara da Niger.
A makonni 41 mutum 417 ne suka kamu Wanda haka ya nuna an samu ragowa a yaduwar cutar idan aka kwatanta da mako na 40 da aka samu mutum 535.
Idan ba a manta ba a watan Satumba hukumar NCDC ta bayyana cewa mutum 46 sun mutu a cikin mako daya a dalilin kamuwa da cutar amai da gudawa a kasar nan.
Rahotan ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe an gano su ne daga jihohi 8 a kasar nan.
Jihohin sun hada da Borno-13, Sokoto-12, Katsina-8, Bauchi-6, Niger-3, Kaduna-2, Adamawa-1 da Kano 1.
Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan
1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.
2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.
3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.
4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.
5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.
6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.
7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.
8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.
9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.
10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.