Jam’iyyar APC a jihar Anambra ta gargaɗi ƴan jam’iyyar APGA ƙarkashin gwamnan jihar Willie Obiano da su shiga taitayin su su daina rikita ke har da labaran karya.
Shugaban yaƙin zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar Anambra, Andy Uba, Afam Ogene ya aika wa ƴan APGA da wannan gargaɗi.
” Kun bi gari kuna yaɗawa wai APC ta rubuta sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 10 wanda ta saka cewa ita ta cinye su kawai don ta kawo ruɗani a ciki jama’a.
” Toh ina so in gaya wa APGA, cewa idan ma hannun ka mai sanda su ke yi son tsoron shan ƙasa, ta sani mu a APC ba zamu lamunci haka ba. Ba za mu ja bakin mu yi shiru ba ana kantara mana karyar da bamu ji ba, bamu gani ba.
” Idan da gaske ne APC ta yi haka, me ya sa APGA bata janye daga zaɓen ba, ai sai ta janye ta ce ba ta yi saboda ta gano wata maƙarƙashiya da ake ƙullawa don a kada ta da karfin tsiya. Amma kuma da ita ake komai, ta koma bayan fage ta ife-ife.
Ogene ya ce ƙuri’un jama’a su zasu tabbatar da sabon gwamna a Anambra ba soki burutsu ba.
Soludon APGA ya lallasa Uba da Valentine a ƙananan hukumomin su na haihuwa
A ci gaba da ƙidayar ƙuri’u da INEC ke yi a safiyar Lahadi da kuma waɗanda aka yi a jiya Asabar, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Charles Soludo ya na kan gaba da tazara mai yawa, inda hatta ƙananan hukumomin gaggan masu ja da shi, Andy Uba da Valnatine Ozigbo sai da ya lashe.
Duk da cewa su ukun kowane ya lashe mazaɓar sa, hakan bai hana Soludo saɓule masu wando a ƙaramar hukumar kowanen su ba.
A Ƙaramar Hukumar Aguata ya yi masu fintinkau, inda su biyun idan aka haɗa ƙuri’un su, ba su kai yawan na Soludo ba.
AGUATA Local Government
In four wards, elections didn’t hold. Umuchu 1 (3 Units – 2292), Igbokwu 1 (3-926) 5 units 2665, Ekwulobia II (2 units)
Registered Voters – 144766
Accredited Voters – 20809
A – 111
AA – 07
AAC – 73
ADC – 32
ADP – 91
APC – 4773
APGA – 9136
APM – 40
APP – 11
BP – 22
LP – 132
NNPP – 11
NRM – 30
PDP – 3798
PRP – 31
SDP – 60
YPP – 1070
ZLP – 120
Ya samu 9,136. Andy Uba na APC kuwa ya samu 4,773. Sai Ozigbo na PDP ya samu 3,778.
Zaɓen dai ya nuna cewa jama’a ba su fito sosai sun jefa ƙuri’a ba.
Daga cikin yawan masu rajistar zaɓe, ƙuri’un da aka jefa sun tabbatar da cewa kashi 20% ne kacal na masu rajista su ka jefa ƙuri’a a ranar Asabar.
Za a ci gaba da jefa ƙuri’a a ranar Lahadi, a sauran wuraren da ba a samu tantance masu jefa ƙuri’a da wuri ba.