Shugaban Kamfanin BUA Abdulsamad Rabiu ya koka a kan tsadar kuɗin dakon kaya daga Legas zuwa cikin sassan Najeriya.
Ya ce kuɗin dakon kaya cike da kwantina daga Chana zuwa Legas, ya fi arha matuƙa fiye da kuɗin dakon kayan daga Legas zuwa Kano, nan cikin Najeriya.
Ya yi wannan bayani ne a wurin taron zuba jari a Paris, babban birnin ƙasar Faransa.
Abdulsamad ya yaba wa gwamnatin Buhari ganin yadda ya farfaɗo da zirga-zirgar jiragen ƙasa, tare da cewa hakan idan aka ƙafa gina wasu titinan, zai samar da sauƙin zirga-zirga a ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga masu zuba jari na ƙasashen waje cewa kamata ya yi su zuba jari a Najeriya, musamman a fannin sufurin jiragen ƙasa.
Sannan kuma ya ce akwai sinadaran haɗa siminti har fiye da tan biliyan 45, kwance a ƙasa babu mai amfana da shi, domin su da ke sarrafa siminti kakaf kamfanonin simintin Najeriya a yi tan miliyan 30 ne a kullum.
Abdulsamad ya ce ya na sayar da simintin sa har a jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, kasar da ta kai tazarar kilomita 400 daga Sokoto, inda ake yin simintin da har ake yin simintin da ya ke fitarwa waje ɗin.
BUA ya ce akwai ɗimbin albarkatun ƙasa kwance a faɗin ƙasar nan, musamman gas da kwal da sauran su. “Amma abin takaici, har ƙarafa sai an shigo da su a Najeriya.
“A duk shekara muna kashe dala biliyan 2.5 wajen shigo da ƙarafa a Najeriya.” Inji shi.