Kotu dake Kasuwar nama dake cikin garin Jos jihar Filato ta yanke wa wani barawon akuya hukuncin dauri na tsawon watanni shida.
Wanda aka daure mai suna Abbas Isaiah mai shekara 25 zai biya tarar naira 15,000 ko kuma ya zarce gidan kaso.
Bayan Isaiah ya amsa laifinsa alkalin kotun Lawan Suleiman ya ba shi zabi, ko ya biya kudin belin naira 15,000 ko ya yi zaman kurkuku na tsawon watanni shida.
Suleiman ya ce ya yanke wannan hukunci ne domin ya zama ishara ga barayi masu sace wa mutane dabbobi a gidaje su shiga taitayin su.
Dan sandan da ya shigar da kara kotu mai suna Monday Dabit ya ce rundunar ta samu labarin abin da ya faru ranar 15 ga Oktoba bayan mai akuyan Nwosoghunnaya Uchechi ya kawo kara ofishinsu dake Anglo-Jos.
” Uchechi ya ce Isaiah ya afka masa gida ya kwance masa akuyar sa dake daure ya yi waon gaba da ita.
Satar akuya da kajin mutane ya zama ruwan dare a unguwanni a garin Jos. Mazauna na kukan cewa kiwo agida na neman ya gagaresu saboda dauke dauken kaji da dabbobi.
Barayin kaji, akuya, bunsuru ko tumakai sukan saida su ne ga mahauta a ba su na kashewa sukuma su saida wa masu cefanen naman miya.