A ranar Litini ne kotun Iyaganku dake Ibadan jihar Oyo ta daure wasu matasa biyu Sodiq Hamzat mai shekara 22 da Taoreed Hamzat mai shekara 22 da laifin kashe wani dan acaba da dukan tsiya.
Kotun ta kama Sodiq da Taoreed wadanda jami’an tara haraji ne na gwamnatin jihar Oyo da laifin hada baki da kuma laifin aikata kisa.
Alkalin kotun Munirat Giwa-Babalola ta yi watsi da rokon sassauci da matasan suka yi cewa matasan za su yi zaman kurkuku har sai kotun ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Za a ci gaba da shari’a ranar 3 ga Fabrairu 2022
Lauyan da ya shigar da karar Oluseye Akinola yace Sodiq da Taoreed sun kashe wani dan acaba mai suna Dare Oyo mai shekaru 25 ranar 10 ga Nuwanba.
Akinola yace a wannan rana Sodiq da Taoreed sun tare Ojo dake kan babur a hanyar Queen Cinema, Adamasingba da misalin karfe 12 na rana don ya siya tikitin Naira 100 da masu abun hawa na haya ke siya kulum.
“Bayan sun tare Oyo sai ya ce ba zai siya tikitin ba saboda bashi da kudi. Fadin haka ke da wuya sai Sodiq da Taoreed suka yi wa Ojo taron dangi suka lakada masa dukan da ta aika da Oya barzahu.
Akinola ya ce hakan da suka yi ya saba wa dokar Criminal Code Cap na jihar Oyo na shekara ta 2000.
Discussion about this post