Babban kotu sauraren kararraki a jihar Legas ta bada belin wani dan kasuwa da aka kama da laifin shigo da jabun kwayoyin Tramadol kasar nan akan Naira miliyan 10.
Hukumar kula da ingancin abinci da magungun ta kasa NAFDAC ce ta shigar da kara a kotun.
NAFDAC ta kama Afamefuna Udensi mai shekaru 43 dake zama a lamba 2 Ezinwanne a Onitsha jihar Anambra ranar 26 ga Oktoba.
Binciken da NAFDAC ta yi ya nuna cewa magungunan jabu ne kuma basu da lambar rajista na NAFDAC.
A zaman da kotu ta yi ranar 15 ga Nuwanba Okpoko ya nemi kotun ta ba Udensi beli.
Lauyan da ya shigar da kara Barthlomew Simon ya ce bai amince kotun ta bada belin Udensi ba saboda zai iya guduwa a nemi shi a rasa.
Osiagor ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 11 ga Fabrairu.
Discussion about this post