Alkaluman sakamakon gwajin cutar korona da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna mutum biyu sun mutu sannan wasu mutum 74 sun kamu da cutar.
Hakan ya nuna an samu ragin mutum 14 daga cikin mutum 89 din da suka kamu ranar Asabar.
Zuwa yanzu mutum 211,962 ne suka kamu da cutar, mutum 203,212 sun warke sannan mutum 5,817 na dauke da cutar.
Mutum 2,896 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Daga ranar Litini zuwa Alhamis din da suka gabata mutum 10 sun mutu sannan mutum 1,218 sun kamu da cutar a kasar nan.
A ranar Litini mutum 771 ne suka kamu sannan mutum 2 sun mutu.
Mutum 159 ne suka kamu, babu wanda suka mutu ranar Talata.
A ranar laraba mutum biyu sun mutu, mutum 116 sun kamu.
Sannan a ranar Alhamis mutum shida sun mutu, mutum 182 sun kamu.
Yaduwar cutar
Legas – 77,770, Abuja-23,261, Rivers-12,678, Kaduna-10,022, Filato-9,756, Oyo-8,742, Edo-6,572, Ogun-5,373, Kano-4,354, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,545, Kwara-3,930, Delta-4,096, Osun-3,006, Enugu-2,761, Nasarawa-2,462, Gombe-2,579, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,017, Imo-2,053, Bauchi-1,681, Ekiti-1,771, Benue-1,809, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,240, Bayelsa-1,240, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-604, Yobe-501, Cross-Rivers-634, Kebbi-458, Zamfara-302, da Kogi-5.
Bayan haka wani ma’aikacin jinya dake aiki da asibitin FMC Keffi jihar Nasarawa Ibrahim Musa ya yi kira ga mutane da su je su yi gwajin cutar korona sannan su rage yawan ziyartar ‘yan Uwa da abokan arziki domin dakile yaduwar cutar.
Musa ya ce ya yi wannan kira ne ganin yadda wasu mutane ke cewan duk da abubuwan da ya faru basu kamu da korona ba.
Ya ce akwai yiwuwar mutum ya kamu da cutar ba tare da ya sani ba saboda babu alamun cutar a jikinsa sannan rashin kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar da ziyartan mutane ka iya yada cutar ba tare da an sani ba.
“Irin hakan be yake bai wa jami’an lafiya wahala wajen gano yadda mutum ya kamu da cutar.
“A dalilin haka nake kira ga mutane da a ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar inda ya kamata a yi amfani da takunkumin fuska a yi amfani da shi inda ya kamata a wanke hannu ko a bada tazara duk a kiyaye.