Bisa ga alkaluman sakamakon gwajin cutar korona da hukumar NCDC ta fitar tsakanin ranakun Juma’a zuwa Litinin mutum 230 suka kamu da cutar sanna 35 kuma suka riga gidan gaskiya.
A ranar Juma’a mutum 16 ne suka mutu, 129 kuma suka kamu da cutar.
Mutum 11 suka mutu, 51 suka kamu da cutar ranar Asabar.
A ranar Lahadi mutum 8 suka mutu, 20 suka kamu da cutar.
Babu wanda aka rasa amma mutum 30 sun kamu ranar Litini.
Zuwa yanzu mutum 213,177 sun kamu, an sallami mutum 205,770.
Korona ta yi ajalin mutum 2,968 a Najeriya.
Yaduwar cutar
Legas – 77,949, Abuja-23,415, Rivers-12,787, Kaduna-10,143, Filato-9,866, Oyo-8,758, Edo-6,598, Ogun-5,374, Kano-4,397, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,573, Kwara-3,930, Delta-4,096, Osun-3,016, Enugu-2,776, Nasarawa-2,517, Gombe-2,695, Katsina-2,317, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,029, Imo-2,053, Bauchi-1,774, Ekiti-1,777, Benue-1,863, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,250, Bayelsa-1,248, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-611, Yobe-501, Cross-Rivers-662, Kebbi-458, Zamfara-331, da Kogi-5.
Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa NPHCDA ta bayyana cewa gwamnati ta yi wa mutum miliyan 5,891,305 allurar rigakafin korona a cikin watanni 8 a kasar nan.
Shugaban hukumar Faisal Shu’aib ya ce mutum 5,891,305 ne suka yi allurar rigakafin cutar zango na faro sannan mutum 3,252,067 ko kuma mutum kashi 2.9% ne suka kammala yin allurar rigakafin cutar zango na biyu.
Ya ce adadin yawan mutanen da ya kamata a yi wa allurar rigakafin cutar a kasar nan sun kai miliyan 111,776,503.
Shu’aib y ace gwamnati na da burin yi wa akalla mutum kashi 50% na mutanen dake zama a kasar nan rigakafin korona nan da watan Janairu 2022.
Ya ce gwamnati bay a ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama da ko yana siyar wa mutane katin shaidan yin allurar rigakafin.
Shu’aib y ace gwamnati ta saka jami’an tsaro a kowani wurin da ake yi wa mutane allurar rigakafin domin tabbatar cewa wadanda suka yi allurar rigakafin ne suke samun katin shaidan yin rigakafin.