Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya koma jami’ar Landan domin Karatun babban Digiri kan shari’ar musulunci.
Khalifah Sanusi ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya tattara yanzu zai koma Landan da zama saboda karatu.
Sarki Sanusi kwararren malamin addinin musulunci ne wanda yayi karatu masu zurfi kan addinin Islama.
Khalifa Sanusi ya yi karatu masu zurfi a harkar hadahadar kudi. Sannan kuma ya samu lambobin yabo na girmawa daga manyan jami’oin kasashen duniya.
Bayan tsige sarki Sanusi daga sarautar Kano, darikar Tijjaniya ta nada shi Khalifar darikar a Najeriya.
Discussion about this post