Ƴan bindiga sun shiga garin Unguwar Dudu suka kashe mutane da dama, waɗanda har zuwa yanzu ba a tantance yawan su ba.
Sun kuma kama wasu mutane tare da kwashe kayan abinci da kayan masarufi ƙarƙaf a garin.
Wannan ne farmaki na biyu da su ka kai yankin, tun bayan harin da su ka kai harin Unguwar Samanja, wanda PREMIUM TIMES Hausa ta buga labari kwanakin baya.
Unguwar Dudu na cikin Ƙaramar Hukumar Faskari, kuma garin ya na kusa da Sansanin Zaratan Sojojin Musamman da ke Faskari, kan hanyar zuwa Gusau daga Funtuwa.
Mohammed Habibu, wani mazaunin Kaduna ya shaida mana cewa shi haifaffen Unguwar Dudu ne, amma an kashe masa kawunnai guda biyu a harin.
“Sai da aka je Gusau aka kira ni a waya aka sanar da ni. Saboda hankali na ya tashi, jin kashe min mutum biyu, ban ma tsaya na tambayi mutane nawa aka kashe ba.
Ya bayyana sunayen mamatan da marigayi Alhaji Ado da marigayi Alhaji Bature.
Jama’a da dama sun daɗe da yin hijira a yankunan Faskari, Sabuwa, Ɗandume, Ƙanƙara Funtuwa, Batsari, Jibiya da Safana, duk a Katsina, mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari.
Makonni biyu ne muka bada labarin yadda mahara su ka hana sallar Asubahi, su ka kashe mutum shida, su ka kwashi mutane a yankin Faskari
ASHAFA MURNAI
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kutsa ƙauyen Unguwar Samanja a daidai lokacin da ake shirin Sallar Asubahi, a ranar Litinin.
An tabbatar da cewa sun riƙa buɗe wa mutane wuta, har su ka kashe mutum shida nan take, kuma su ka arce da wasu a matsayin sun yi garkuwa da su.
Unguwar Samanja ta na kusa da garin Daudawa a Ƙaramar Hukumar Faskari.
Daudawa can ne aka haifi marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Umaru ‘Yar’Adua, lokacin da mahaifin sa ya je aiki can daga Katsina.
Jihar Katsina can kuma ne mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari. Amma matsalar tsaro ta yi wa jihar ɗaurin-gwarmai, ta gagari waɗanda haƙƙin shawo kan lamarin ya rataya a wuyan su.
Wasu mazauna garin Daudawa da ke kusa da Unguwar Samanja inda aka kai farmakin, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun isa Unguwar Samanja wajen ƙarfe 5.49, kuma a kan babura su ka je, kowane ɗauke da muggan makamai.
Sun isa a lokacin da ake ta shirye-shiryen alwalar Sallar Asubahi.
Ita ma ƙaramar hukumar Faskari ta sha fama da ‘yan bindiga tsawon shekaru.
Kuma ta na cikin Ƙananan Hukumomi 13 da aka yanke wa hanyoyin sadarwar waya a jihar Katsina.
Wata ƙungiya a cikin garin Daudawa ta yi kukan cewa duk da matakan tsaron da ake cewa ana ɗauka, har yau ba a daina kai hare-hare a yankunan Ƙaramar Hukumar Faskari ba.
Wani mazaunin Daudawa mai suna Nasir Hassan, ya ce ‘yan bindigar sun dira ƙauyen a kan jerin-gwanon babura, inda su na shiga garin su ka riƙa darzaza harbin bindigogi, duk aka ruɗe.
“Daga sahihin labarin da na ji, sun kashe mutum biyar, waɗanda aka rufe yau Litinin.”
Hassan wanda ɗalibin gaba da sakandare ne a wata makaranta a jihar Zamfara, ya ce “maharan sun kuma ƙone gidaje, sun ƙone shagunan sayar da kayan abinci da kayan masarufi.
“An shaida min cewa ba su kwashi kayan kowa ba, sun dai kona shagunan sayar da kayan abinci da masarufi.”
Amma wani mai suna Auwal Liman, wanda shi ma mutumin Daudawa ɗin ne, ya shaida wa wakilin mu cewa waɗanda aka kashe sun fi mutum shida, domin a daidai shiga garin Unguwar Samanja ma maharan sun harbe wani mutumin Unguwar Labbo.
Bahisulhaq Alhassan wanda ɗalibi ne a Faskari, ya shaida wa wakilin mu cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe ɗin ma abokin sa ne mai suna Ja’afar Kabir can a Unguwar Samanja ɗin.
Wakilin PREMIUM TIMES ya kira lambar Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, amma bai ɗauki waya ba. Kuma ya tura masa saƙon tes, shi ma bai maida masa amsa ba.
Discussion about this post