Cibiyar Horas da Hafsoshin Najeriya (NDA), ta nemi Majalisa ta amince domin ta kashe Naira miliyan 300 a ranar faretin yaye sojoji na shekarar 2022.
Wannan roƙo na cikin bayanin da Babban Kwamandan NDA Ibrahim Yusuf ya karanta s gaban Kwamitin Majalisa Tarayya Kan Tsaro, a ranar Laraba.
Bikin yaye ƙananan hafsoshin dai, wato ‘Passing out Parade’, biki ne da NDA ke shiryawa duk shekara a Kaduna, idan za yaye sojojin da ta horas. Kuma Shugaban Ƙasa na halarta a duk shekara.
NDA ta bayyana wa Kwamitin Tsaro cewa an yi rafkanuwa ne ba a saka waɗannan kuɗaɗe naira miliyan 300 a cikin kasafin 2022 na naira biliyan 22.7 da NDA za ta kashe ba.
A kan haka ne ya bijiro da roƙon Majalisa ta amince a saka adadin kuɗaɗen a cikin kasafin na 2022.
Idan ba a manta ba, watanni biyu baya ‘yan bindiga sun kutsa cikin gidajen kwanan sojoji a NDA har su ka yi kisa, kuma suka arce da wani jami’in soja.