Kusan makonni biyu da suka shige, an cika duniyar soshiyal midiya da wani bidiyon da aka nuno wani farin ƙyallen yadi ya na filfilawa daga sama ya na saukowa ƙasa a cikin gari.
Lamarin ya faru ne a cikin wani gari a Jihar Ondo. An nuno mutane na ta hargowar murnar ganin yadda ƙyallen mai tsaro yadi 120 ke filfilowa ƙasa, kowa na jiran ya kai hannun sa idan ya sauko, domin samun tubarraki.
A zaton mutanen, ƙyallen wata karama gare shi, domin gani suke yi daga sama ya sauko, ko kuma daga sama aka sauko da shi domin jama’a su samu falala ko wata karama.
Bayan saukar ƙyallen, jama’a sun yi dafifi a ƙofar gidan Alhaji Yesufu, cikin unguwar Sabo, a jihar Ondo inda ƙyallen ya sauka, a ranar 27 Ga Oktoba.
Gaskiyar Abin Da Wakilin Mu Ya Gano A Garin:
Wakilin mu ya je har Sabo, kuma da farko ya samu wata mata mai suna Fatima Yesufu, wadda aka yi komai a kan idon ta.
“To ni dai ina cikin gida sai na riƙa jin hayaniyar mutane ta kaure. Na fito na ga an yi dafifi su na ta kiciniyar kokawar yankan wani faskeken ƙyalle.”
Haka wannan gyatumar ta shaida wa wakilin mu, kuma ta ce ƙyallen a gidan ɗan ta ya sauka.
“Mutane da yawa ma tsalle suka riƙa yi su na afkawa cikin gidan, duk dai don su kai hannun su ga wannan ƙyalle.
“An yi ƙoƙarin a kore su, amma sai ƙara tuɗaɗowa suka riƙa yi. Wuri ya kaure da tirmitsitsi. Sai da ta kai na koma gefe ina kallo, don kada a tattake ni.” Inji gyatumar.
Shi ma Babangida Usman ya ga duk abin da ya faru, saboda ya na zaune ne a gidan da ke kallon gidan Alhaji Yesufu, inda ƙyalle ya sauka.
“Ni ne kat, domin da ni aka yi kokawar yankar ƙyallen domin samun tubarraki.
“Ai ina faɗa maka duk wani wanda idon sa ya gane masa ƙyallen tun a sama, sai da ya biyo har nan unguwar Sabo, inda ƙyallen ya sauka, a gaban gida na. Kuma a gaban ido na. Ni ma na bazama na shiga cikin tirmitsitsin masu yankar ƙyallen domin neman tubarraki ko falala.”
Jahilci Ya Fi Hauka Wuyar Magani:
Babangida ya shaida wa wakilin mu cewa ai ba a gama watsawa daga wurin yankar ƙyallen ba, sai ga wata mata, wadda ke sana’ar shirya wurin taro ko biki, ta zo ta ce ai ƙyallen ta ne da za ta ɗaura a wurin wani taro, shi ne iska ko guguwa ta ɗauka, ta yi sama da shi.
Matar ta ce adon ƙayatar da wurin taro za ta yi da ƙyallen, amma sai ta neme shi ta rasa, iska ya yi sama da shi.
“Na ɗan yi masa kwalliya ce, sai na ɗan shanya shi domin ya bushe tun jiya. Amma sai na neme shi na rasa.”
Matar dai a lokacin da ta ke wannan bayani, an rigaya an yagalgala ƙyallen yadin, kowa ya yanki rabon sa.
Yayin da matar ta haƙikice cewa sai an biya ta kuɗin ta Naira 50,000 da ta sayo yadin har 120 a Legas, an shawarce ta kawai ta haƙura, ta ɗauki asara. Tunda ba wanda ya san yawan mutanen da suka yanki yadin, kuma duk kowa ya kama gaban sa.
Fallen Yadi Na Ne, Ba Shi Da Tubarrakin Komai -Agnes Fadoju:
Wakilin mu ya yi tattaki har wurin Agnes Fadoji, inda ta bayyana masa cewa Naira 50,000 cur ta sayo shi a Legas, kuma bandir ɗaya ne mai yadi 120.
“Na sayo shi domin na ƙawata wurin taro da shi.”
Ta ce duk da dai ta ɗibga asara, amma ta na farin ciki, domin a yanzu ta yi suna, jama’a sai tururuwa suke yi wurin ta. Kuma hakan ya sa’an ƙara sanin irin sana’ar da ta ke yi.
Daga nan Agnes ta nuna wa wakilin mu irin yadin da kuma inda ta ke shanya su bayan an rangaɗa masu rubutu.
“A ranar Talata ce ni da yara na muka wanke yadin muka shanya. Kuma ba ma shi kaɗai ne muka shanya ba. Washegari ranar Laraba, na duba inda na yi shanya amma ban ga alamun wani abin al’ajabi ba. Kuma ban fahimci babu wani yadin ba.
“Sai can da rana tsaka aka fara kira na wai ko na shanya ƙyallen da ban gani ba? Na ce masu ƙwarai, ban ga guda ɗaya ba kuwa. Na kira miji na, ya ce min ai da iska ya ɗauki ƙyallen, ya filfila shi cikin unguwar sabo, inda aka riƙa rububin yankan sa, ana zaton ɗauke ya ke da kamara daga sama. Wai jama’a sun kwashi tubarraki a jikin ƙyallen.
“Ina zuwa unguwar Sabo, na ga mutane kowa ya ɗaura ƙyallen yadin da ya yanka a ƙugun sa. Wai neman tubarraki.”
“Ga shi fa an rubuta sunan kamfani na ‘HOSSANA’ a jikin ƙyallen, amma duk ƙoƙarin da na yi wa jama’a domin nuna masu cewa nawa ne, ko kula ni ba su yi ba.”
Agnes ta ce a ƙarshe an ɗunguma an tafi gidan Seriki na Sabo, “ya shaida min cewa idan da na ga irin yadda yadin ya riƙa saukowa daga sama, ni ma cewa zan yi yadin karama ya ke ɗauke da ita.”