Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya jinjina wa jaridar PREMIUM TIMES kan kaddamar da littafi da tayi kan tarihin Daular Usumaniyya, wanda Farfesa Murray Last ya rubuta.
An kaddamar da wannan littafi a garin Sokoto jihar Sokoto kuma ya samu halartar manyan ‘yan Najeriya har da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ranar Litinin, 1 ga Nuwamba.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin, Sultan Sa’ad ya ce ya samu shakku da farkon lokacin da PREMIUM TIMES iske shi da wannan magana.
” Dalilin da ya sa na samu shakku a akai kuwa shine bana son in fada cikin wani abu mai kama da satar fasahar wani da zai jawo cecekuce akai. Sai na umarci a bani lambar wayar faefesan in yi magana da shi da kai na. Da muka yi magana sai ya ce tabbas shi ne ya amince PREMIUM TIMES ta buga wannan littafi kuma ta yada shi. Daga nan sai na amince a ci gaba da wannan shiri da ake na kadda amar da littafin.
” PREMIUM TIMES kun yi abin azo a gani. Daular Usumaniyya na farinciki da alfahari da abin da kuka yi na yada tarihin kasar mu ta hanyar buga wannan littafi. Ba za mu manta da ku ba, kuma da ga yanzu za mu saka ku a kan gaba wajen yada manufofin mu da ayyukan wannan daula.
Haka nan shima gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya gode wa PREMIUM TIMES kan wannan kokari da ta yi na wallafa wannan littafi da kaddamar da shi.
” Muna godiya ga Farfesa Murray da Jaridar PREMIUM TIMES. Wannan abu ne da ba za a manta da shia tarihi ba. Wannan jarida ta yi taka rawar gani.
Discussion about this post