Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano ta bayyana takaicinta kan halin da ɗaliban jihar Kano da suka rubuta jarrabawar NECO ke ciki, sakamakon rashin biyan kuɗin da Gwamnatin Kano ta ki yi.
Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano, Bashir Sanata, yace yanzu haka waɗannan ɗalibai na gab da rasa gurbin karatun da suka samu.
Sanata yace wannan abin Alla-wadai ne, kuma abin kunya ne, yadda wannan Gwamnati ta kasa inganta ɓangaren ilmi.
“Duk da jama’ar Kano basu manta gangamin da Gwamna da iyalin Gwamna da Makusantansa suka yi wata biyu da suka wuce don zuwa ƙasar Birtaniya murnar kammala karatun Ɗan Autan Gwamna ba. Amma Gwamnati ta gagara biyan kuɗin makaranta da bai taka kara ya karya ba ga ‘ƴa’ƴan talakawan jihar.
“Ɗalibai da iyayensu a jihar Kano na cikin damuwa, sakamakon yadda wannan Gwamnati ta yiwa ilimi ƙanshin mutuwa.
“Jam’iyyar PDP na ƙara tunatar da wannan Gwamnati cewa, ilimi shi ne tushen rayuwa, kuma shi ne babban abin da al’ummar mu suke buƙata a inganta.
“Shin ina ƙanzon kurege da hayagagar da wannan Gwamnati ke yi game da ilimi?
“Shin Gwamnatin Kano tana tunanin halin da waɗannan ɗalibai za su shiga idan suka rasa gurbin karatu?
“Wane tanadi Gwamnatin ta yi musu, matuƙar ta hana su samun makaranta? Inji Kakakin na PDP Bashir Sanata.
PREMIUM TIMES tayi kokarin ji ta bakin hukumomin illimi a Jihar ta Kano amma abun ya ci tura.