Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa zuwa yanzu dai an yi wa mutum 3,899,238 rajista ta yanar gizo a faɗin ƙasar nan.
Cikin wata sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa zuwa yanzu jihar Ogun ce kan gaba wajen yawan mutanen da su ka yi wannan rajista, har mutum 453,949.
Jihar Delta ke biye da Ogun, inda aka samu mutum 297,396 sun yi rajista ta yanar gizo.
Jiha ta uku kuwa ita ce Bayelsa, wadda aka samu mutum 252,534 su ka yi wannan rajista.
Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas ce ta ƙarshe a jerin yawan rajista a jihohin Najeriya. An samu mutum 18,000 kacal a Yobe.
Sauran jihohin da ke bi wa Yobe a ƙarancin yawan masu rajista, sun haɗa da Abia mutum 19,308, sai kuma Kebbi mutum 23,758.
Jihar Filato: INEC Ta Yi Wa Mutum 30,449 Rajistar Zaɓe:
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa mutum 30,449 rajistar yin zaɓe a Jihar Filato a cigaba da ta ke yi na gudanar da aikin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar nan, wato Continuous Voter Registration (CVR), wanda aka fara yi a ranar 28 ga Mayu.
Malam Halilu Pai, kwamishinan zaɓe mai zama a jihar, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Jos, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai kan watanni uku na farko na wannan shekarar.
Pai ya ce a cikin wannan lokacin, mutum 111,276 masu yin rajistar zaɓe ne su ka nemi yin rajistar.
A watanni uku na farkon shekarar aikin rajistar masu zaɓen, mutum 88,573 ne su ka nemi yin rajista, kuma 24,654 aka yi wa rajistar, inji shi.
Haka kuma katin masu zaɓe (PVC) guda 1,524 ne aka musanya, yayin da katin zaɓe 13,898 ne aka yi wa tiransifa zuwa sabon wurin da masu zaɓe su ka koma.
Ya ce, “A wa’adin watanni uku kashi na biyu na shekara, waɗanda ya ƙare a ranar Juma’a, 29 ga Oktoba, mutum 21,001 su ka nemi yin rajista, aka yi wa 4,653 rajistar, aka musanya katin zaɓe guda 6,66, sannan aka yi wa 3,347 tiransifa zuwa sabon wurin da masu zaɓe su ka koma da zama.
Kwamishinan ya ce a ƙoƙarin da hukumar ke yi na yi wa ‘yan Nijeriya aiki tuƙuru a wajen yin wannan rajista, ta kafa gidan yana na musamman, wato: cvr.inecnigeria.org.
A cewar sa, an yi gidan yanar ne saboda sababbin masu son yin rajista da waɗanda ke da rajistar su fara rajistar a intanet ta hanyar cike fom da tura shi tare da hoton su idan sun ƙare.
Ya ce daga nan za su nuna buƙatar su a gidan yanar ta a ba su rana da lokacin da za su ziyarci ofishin INEC na jiha ko ƙaramar hukuma domin a kammala yi masu rajistar ta hanyar ido da ido inda za a ɗauki zanen yatsan su.
Duk waɗanda su ka riga su ka yi rajista a matsayin masu zaɓe su ma za su iya zuwa su gudanar da waɗansu ayyukan na yin rajista, misali tiransifa, gyara a bayanan su da kuma musanya katin zaɓe da ya yi dameji ko ya lalace ta hanyar yanar gizo.
Ya ce, “Ana fatan cewa ta hanyar wannan gidan yana za mu rage cinkoson mutane a cibiyoyin yin rajista , musamman da yake har yanzu ana fama da annobar korona (COVID-19), don a sauƙaƙa yin rajistar, a ba ‘yan Nijeriya kyakkyawar damar shirya wa yin zaɓe.
“A lura da cewa rajista ta hanyar yanar gizo kyauta ake yin ta, babu wani shagon da za a ce shi ne INEC ta yarda da shi kuma babu katin kuɗi da ake saye domin yin rajistar ta hanyar yanar gizo.”
Pai ya tabbatar wa da masu so su yi rajista da cewa ban da yin rajista ta hanyar gidan yana, jama’a za su iya takawa da ƙafar su zuwa kowace cibiya inda za a yi masu rajistar.
Ya ce za a ci gaba da gudanar da wannan aiki har zuwa wajen watanni uku na kashi na uku na shekarar 2022.
A cewar sa, saboda haka akwai isasshen lokaci da hukumar za ta kai kowane lungu da saƙo na jihar.
Ya ce, “A kan haka, bari in tabbatar wa da dukkan mazauna Filato cewa babu wanda ya cancanci yin rajista da za a ware ko a ina ya ke zaune ko kuma wani halin rayuwa da ya ke ciki.
“Zan nanata cewa aikin rajistar katin zaɓe na ‘yan Nijeriya ne da ke cikin waɗannan rukunnan: waɗanda su ka cika shekara 18 da haihuwa zuwa sama kuma ba su yi rajista ba.
“Akwai kuma masu zaɓe waɗanda su ka yi rajista kuma su ka samu matsala da rajistar su a lokacin tantancewa a zaɓuɓɓukan baya ko dai da katin su ko na’urar yin rajista ta kasa ɗaukar zanen yatsan su, da kuma waɗanda su ka yi rajistar amma su na so a yi masu tiransifar wurin kaɗa ƙuri’ar su zuwa wani wurin daban.
“Haka shi ma wanda ya yi rajista amma ya na so ya gyara wani abu a cikin bayanan sa kamar rashin rubuta suna daidai da kwanan watan ranar haihuwa.”
Discussion about this post