Bisa ga sakamakon Zaben da aka bayyana na ƙananan hukumomin jihar 21 Charles Soludo na jam’iyyar APGA ne kan gaba innda ya lashe kananan hukumomi 18 cikin su.
Alkaluman sakamakon sun nuna cewa kuri’un da ke tsakanin Soludo da Ozigbo na PDP akwai kuri’u sama da 45,000.
Abin da ya sa aka kai ga sanar da zaɓen INKONKULUSIB’ a wannan zaɓe shine malamin zaɓen karamar hukumar Ihiala ya sanar cewa ba a yi zaɓe ba a karamar hukumar. Kuma akwai masu zaɓe sama da mutum 150,000.
A dalilin haka an bayyana zaben bai kammalu ba.
A wajen bayyana sakamakon zaɓen an rika samun matsaloli game da Alkaluman da aka kawo daga rumfunar zaɓe.
An yi ta dakatar da bayyana sakamakon zaben saboda ayi gyararraki ga alkaluman da wakilan zabe suka zo da su.
Malamar Zabe Florence Obi, ta ce sai an yi zaɓen Ƙaramar Hukumar Ihiala da ke da masu zaɓe sama da mutum 150,000 sannan a haɗa alkaluma da aka bayyana da na baya a lissafa kafin nan a faɗi wanda ya yi nasara a zaben.
Discussion about this post