Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya sake buɗe titin da ya tashi daga garin Bama zuwa Banki, bayan Boko Haram sun hana bin titin tun daga 2012, tsawon shekaru 9 kenan.
Titin mai tsawon kilomita 65, shi ne kuma ya haɗe kan iyakar Najeriya da Kamaru a garin Banki. Kuma daga can ne ya haɗa Kamaru da ƙasashen Afrika ta Tsakiya.
Da ya buɗe titin, Zulum ya bai wa Sojojin Operation Haɗin Kai’ motocin sintiri guda 10 domin gudanar da tsaro a kan titin.
Yayin da ya ke damƙa motocin ga Babban Kwamandan Operation Haɗin Kai’, Manjo Janar Musa Christopher, Gwmna Zulum ya yi gargaɗin cewa kada a riƙa karɓar kuɗi ga matafiya masu bin hanyar, kuma kada sojoji su yi amfani da motocin wajen yin sumogal zuwa cikin Kamaru ko kan iyaka.
An yi ƙwarya-ƙwaryan bikin buɗe titin a Mahaɗar Titin Bama zuwa Banki a ranar Laraba.

Discussion about this post