Akalla mata 7 ne suka rasa rayukan su a haɗarin jirgin ruwa da ya auku a kogin da ya ratsa ta kauyukan Gasanya da Gafasa a jihar Jigawa.
Majiya ta bayyana wa BBC Hausa cewa jirgin ruwan ya kife bayan ya dauko fasinjoji 12 daga kauyen Gasanya zai kai su kauyen Gafasa.
Gafasa kauye ne dake karkashin karamar hukumar Kafin Hausa, Gasanya kuma kauye ne dake karkashin karamar hukumar Auyo.
Jirgin ya dauko mutanen bayan an tashi taron Maulud da aka yi a Gasanya.
Wata mata wacce ta rasa ƴarta a haɗarin jirgin Mikail Jibril ta bayyana cewa fasinjojin dake jirgin na ba su wuce ƴan shekaru 11 zuwa 12.
“Mutum bakwai daga cikin fasinjoji 12 dake jirgin ruwan sun mutum sannan an ceto mutum 5.
Dagacin kauyen Gafasa Adamu Abdullahi yace an yi jana’izar mutum 7 din da suka mutu bisa ga koyarwar addinin musulunci.