Gidauniyar Tony Elumelu Foundation ta raba wa masu ƙananan sana’o’i dala $5,000 ga kowane mutum ɗaya, ga mutum fiye da 4,900 a cikin ƙasashe 54 na Afirka.
Gidauniyar Tony Elumelu wadda ke sahun gaba wajen bayar da tallafin koyon sana’o’i ga matasan Afrika, ta bayyana cewa waɗannan kuɗaɗe na tallafin shekara ta 2021 ne, kamar yadda gidauniyar ta saba yi duk kowace shekara.
An tsamo masu ƙananan sana’o’in su fiye da 4,900, daga cikin waɗanda suka cika fam ɗin neman tallafin su fiye da 400,000.
Kuma an zaɓi ne daga kowace ƙasar Afrika a cikin ƙasashe 54, bisa cancanta da gamsarwa kan yanayin sana’ar da za a yi da kuɗaɗen, ko kuma irin sana’ar da ake yi, wadda mai yin sana’ar ya cancanci ta tallafa masa.
Tony Elumelu ya bayyana cewa an tallafa masu ne domin samar da faɗaɗɗar hanyar rage talauci da kuma samar da aikin yi ga ɗimbin al’ummar nahiyar Afirka.
An raba kuɗaɗen ne ga sabbi da kuma waɗanda su ke suka daɗe a cikin sana’a su samu samu jari.
Waɗanda suka yi jawabai a wurin taron sun haɗa da wakilin Hukumar UNDP, Ahunna Eziakonwa da kuma wakilin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), Koen Doens.
Hauwa Liman, wadda ta na ɗaya daga cikin waɗanda suka fara cin moriyar Tallafin Gidauniyar Tony Elumelu cikin 2015, ita ke da kamfanin kasuwancin Africa Abaya a Kaduna.
A wurin taron ta bayyana irin fa’ida da nasibin da ta samu sakamakon tallafin karin Gidauniyar Tony Elumelu.
“Fa’idar ba a jarin da ake ba ka kaɗai ta tsaya ba. Na ƙalu da ilmin sana’a sosai wanda gidauniyar ta horas da ni.”
Gidauniyar Tony Elumelu ta na bayar da tallafin ne duk shekara ta waɗanda su ka cancanta a faɗin Afrika.
A wannan shekarar, Tony Elumelu ya ce kashi 68% na waɗanda za su ci moriyar jarin da kuma horaswa, duk mata ne, wato fiye da mace 2,400 kenan.