Gidauniyar ‘Smile Attract Smile (SAS)’ ta tallafa wa mata zawarawa 105 a babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban kungiyar Bukola Adewumi ta sanar da haka a taron tallafawa zaurawa mata da gidauniyar ta yi a Abuja ranar Lahadi.
Bukola ta ce gidauniyar ta yi hakane domin ganin ta kawar da yunwa da tallauci a tsakanin zawarawa mata.
Ta tabbatar cewa gidauniyar za ta ci gaba da mara wa zaurawa mata baya domin ganin sun zama mutanen da za su iya cin gashin kansu.
“Burin gidauniyar shine tallafawa rayuwar zaurawa ta hanyar basu jari da horar da su sana’o’in hannu.
“Shekaran 2022 gidauniyar na da burin horar da bai wa zaurawa 500 kudaden jari a Abuja.
“Babban burin gidauniyar shine karfafa gwiwowin zaurawa mata kan mikewa su yi aiki ko sana’a domin ciyar da ‘ya’yan su a maimakon yin maula da roko.
Baya ga haka gidauniyar ta taimaka wajen biyan kudin makarantar yara da kudin asibitin yaran da iyayensu zaurawa suka ƙasa biya.
Gidauniyar ta Kuma raba kayan sawa da abinci wa zaurawan a taron.
Evelyn Samson, Cordelia Anyanwu, Abigail Bello da suka amfana da tallafin sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika tallafawa zaurawa mata domin yin haka zai taimaka wajen kawar da yunwa da tallauci a tsakanin su.
Discussion about this post