Babbar Kotun Shari’a da ke Kaduna ta yanke hukuncin kamfanin jaridar Today ta biya gwamnan Kaduna zunzurutun kuɗi har naira miliyan 10 diyyar yi masa ƙazafi da jaridar tayi masa.
Jaridar ta buga labari a 2015 cewa wai gwamna El-Rufai ya bayyana makudan kuɗi har naira biliyan 90 da wasu kantama-kantaman gidaje har 40 a matsayin kadarorin da ya mallaka kafin ya zama gwamna.
Bayan buga wannan labari El-Rufai bai yi wata-wata sai ya garzaya kotu yana ƙalubalantar wannan labari cewa ƙazafi aka yi masa amma bai bayyana abinda jaridar ta rubuta ba wai ya mallaka.
Daga nan aka shiga zaman kotu har zuwa yau da aka yanke hukunci.
Alkalin Kotun maishari’a M L Mohammed ya bayyana cewa bayan nazari da binciken da kotu ta yi da kuma sauraren duka ɓangarorin, ta gano cewa an kantara wa wa El-Rufai shirgegen karya ne da kuma yi masa kazafi na babu gaira babu dalili.
Hakan yasa bayan nazari da kotu tayi ta yanke hukunci kamar haka,
1 – Kamfanin jaridar Today zai biya gwamna El-Rufai zunzurutun kuɗi har naira miliyan 10 diyyar yi masa ƙazafi da aka yi.
2 – Jaridar zata buga mukala a jaridu na tuba da neman yafiya daga gwamnan, da kuma alkawarin ba zata sake aikata irin haka ba.
3 – Sannan kuma da jan kunnen kada ta kuskura ta sake nufin gwamnan da cin mutunci irin haka.