Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya Isiaka Amao, ya bayyana cewa sojojin saman ƙasar nan sun kai hare-hare sau 3,700 a Arewa maso Gabas.
Amao ya yi wannan iƙirarin a ranar Talata, inda ya ce tsakanin watan Janairu zuwa yanzu, an shafe sa’o’i 7,000 ana aiki da jiragen yaƙi a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Air Marshal Amao ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke kare kasafin Sojojin Saman Najeriya, a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Sojojin Sama.
“Tsakanin Janairu zuwa yau ɗin nan, an shafe sa’o’i 7,000 tsakanin tashi da saukar jiragen yaƙi. Kuma duk waɗannan zirga-zirga ɗin akasari hare-hare ne aka kai a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.” Inji shi.
Sai dai kuma duk da wannan iƙirarin na Amao, cikin makon da ya gabata an kashe mutum 44 a Arewa maso Yamma, cikin su har da babban sojan da ya yi ritaya, Sir Marshal Muhammad Maisaka.
A Arewa maso Gabas kuma an kashe mutum 19, ciki har da Burgediya Janar Dzarma Zirkusu.
Kwanan nan Ɗan Majalisar Tarayya Isa Jaha, ya ce akwai matsala dangane da irin salon yaƙin da Sojojin Najeriya ke yi da Boko Haram ba wanda zai sa a yi galaba a kan su ba ne.
Ya ce a kullum sojojin Najeriya ba su zuwa su yi tattaki har maɓuyar Boko Haram da ISWAP su ragargaje su.
Ya ce sai dai idan su Boko Haram ko ISWAP ɗin ne su ka kawo wa sojoji farmaki, ko kuma suka kai farmaki wani gari, sannan sojojin Najeriya ke ita tarar ‘yan ta’addar.
Amao ya shaida wa Kwamitin Majalisa cewa Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta ƙaddamar da jirgin yaƙi guda ɗaya, samfurin MI171 daga Rasha, sai kuma wasu guda uku samfurin GF 17 daga Pakistan da kuma jiragen yaƙi 12 samfurin 12 A 29 Super Tunaco daga Amurka.”
Ya ƙara da cewa an tura sojojin sama 400 domin samar da tsaro a lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra.
Sai dai kuma Amao da sauran ‘yan kwamitin sun garƙame ƙofa domin ganawar sirri kafin ya gabatar da kasafin kuɗin Sojojin Sama na 2022.
Discussion about this post