Wasu gaggan ɓarayi sun ɓarka ofishin Babbar Mai Shari’a ta Jihar Ogun, Mosumola Dipeolu, suka kawace ilahirin na’urorin da ake yin taron daga nesa, wato ‘virtual’ da kuma ‘Zoom’.
Mosumola ɗin ce da kan ta ta bayyana haka a ranar Talata, yayin ƙaddamar da taron sanin makamar aikin fasahar ICT, wanda ta ce zai taimaka wajen gaggauta yanke hukuncin tulin shari’un da ke gaban kotunan jihar Ogun.
Babbar Mai Shari’a ta ce an kafa na’urorin ne bayan ɓarkewar cutar korona.
“An kafa su ne sakamakon ɓarkewar korona, aka riƙa amfani da su ana taruka da ayyukan kotu daga gida, ta ‘virtual’ da ‘zoom.
“Mun nemi Gwamna Dapo Abiodun ya sanar mana hanyoyin da za a riƙa gudanarwa da aiwatar da ayyukan kotu da sauran tarukan mu da alƙalai. Kuma gwamnan ya amsa da gaggawa ya samar mana dukkan kayan da ake bukata.
“Na riƙa yin taro daga ofis ko daga gida ta hanyar amfani da kwamfuta. Su kuma sauran alƙalai su na yi daga garuruwan su. To katsahan wata rana ɓarayi suka je, suka ofis ɗi na, suka kwashe kayan ƙarƙaf. Yanzu ni ma dai da kwamfuta ‘laptop’ na ke iya shiga tsron.”
Mai Shari’a ya bayyana cewa akwai matuƙar buƙatar fasahar ICT domin a riƙa gudanar da ayyukan shari’a cikin sauri.