Boko Haram ba su daina cin karen su ba babbaka ba har a kusa da Buratai, garin haihuwar tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai.
Wani bidiyo da ‘yan ta’addar su ka saki a ranar Lahadi, sun nuno mutane huɗu da su ka kama a ranaku daban-daban, kuma a wurare daban-daban.
Daga cikin kamammun, biyu an kama su ne a tsakanin garin Buratai Buni Yadi a Jihar Barno.
A cikin an bidiyon wanda aka nuni su ɗaya bayan ɗaya su na magana, inda kowane ya faɗi aikin sa da inda aka kama shi da kuma ranar da aka kama shi, ba a bar kowanen su ya yi roƙon a ceci shi ba.
Wani mai suna Zakariya Azirkime, ya shaida cewa shi ma’aikacin Hukumar UNICEF ne, kuma an kafa shi a tsakanin Maiduguri zuwa Damboa.
Yayin da mutum biyu aka kama su kusa da Buratai, cikon na huɗun mai suna Yusuf Nasiru Kiru kuma ya ce shi ma’aikacin Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa ne (FRSC) daga Kano, kuma an kama shi kan hanyar Kano zuwa Maiduguri.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama kusa da Buratai sunan sa Imran Mohammed Askira, wanda ya ce ya na sana’ar kiwon kaji a gidan gona, kuma ya na yi wa NDA kwangiloli. Bai dai bayyana irin kwangilar da ya ke wa Makarantar Horas da Hafsoshin Sojoji ɗin ba.
Shi kuma ɗayan mai suna Mohammed Askira, ya ce ya taɓa yin aiki a bankin Premier Commercial Bank na Maiduguri, shi ma a kusa da Buratai aka kama shi.
Tun a ranar Lahadi 21 Ga Nuwamba da aka saki bidiyon, jama’a da dama a shafin sada zumunta na Facebook sun cika da alhinin kama Mohammed Askira, wanda sananne ne a shafin Facebook, har a idon wasu ‘yan jarida a Arewa.
Idan ba a manta ba, tun farkon 2017 Buratai ya fara cewa sun gana da Boko Haram.
Lokacin da sojoji su ka shiga Dajin Sambisa, sun ƙudunduno littafin Sahih Buhari su ka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari, aka ce masa Alƙur’anin da Shekau ya gudu ya bari ne.