Yayin da ya ke yanke wa tsohon shugaban Hukumar Gyaran. Fansho Abdulrasheed Maina hukunci, Mai Shari’a ya ce bankunan UBA da Fedility Bank sun miƙa wuya Maina ya yi amfani da su wajen satar maƙudan kuɗaɗen da haƙƙin ‘yan fanshon Najeriya ne.
Mai Shari’a ya ce kuɗin da Maina ya sata ya yi sanadiyyar kassara gidajen ɗimbin jama’a tare da talauta masu haƙƙin karɓar fansho.
Dalilin haka ne ya bayyana cewa kamata ya yi a hukunta bankunan tare da Maina, domin su ne su ka karɓi ajiyar kuɗaɗen satar suka ɓoye masa.
“Kamata ya yi a ce an shigar da Bankin UBA da Fedility Bank ƙara a lokaci ɗaya da Maina.”
Abang ya ƙara da cewa “kamata ya yi a ƙwace lasisin UBA da na Fedility.”
“Waɗannan bankuna sun taimaka wa ɓarawon kuɗaɗen gwamnati ya ɓoye kuɗaɗen da ya sata, ya bar ɗimbin masu haƙƙi kan kuɗaɗen cikin baƙin talauci, wasu har ma suka mutu ba su ci moriyar haƙƙin na su ba.
“Shi kuma Maina ya na can sai ɓalle-bushasha ya ke yi, ya na sayen maka-makan gidaje a Dubai da kuɗin da kowa ya san ba daga haƙƙin albashin da ake biyan sa ba ne.”
Maina Ba Shi Da Imani, Ba Shi Da Tausayi -Mai Shari’a
Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a ya kira Maina, “mutumin da ba shi da imani, babu tausayi ko kaɗan a zuciyar sa, tunda har ya kwashe sama da Naira biliyan 2 na ‘yan fansho shi kaɗai.
Mai Shari’a ya ce babu ta yadda za a yi Maina ya samu Naira biliyan 2, domin albashin sa na matsayin sa na ma’aikatacin gwamnatin tarayya, kaɗan ya zarce naira 300,000 a duk wata.
“Kai ko da shekaru 35 ya yi ya na tara albashin, ba ya taɓa komai a cikin kuɗin, babu yadda za a yi ya tara naira biliyan 2.1.”
Premium Times Hausa ta kawo labarin yadda kotu ta ɗaure Maina shekaru 8 a kurkuku, bayan an samu sama naira biliyan 2 a hannun sa.
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ɗaure Abdulrasheed Maina shekaru takwas a kurkuku, bayan samun sa da laifin wawurar fiye da naira bikiyan biyu daga asusun ‘yan fenshon Najeriya.
Maina wanda Mai Shari’a Okon Abang ya ce ya saci kuɗaɗen a lokacin da ya ke Shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho (PRTT), an kama shi da laifi a tuhumoni masu lamba 2, 6, 9, 3, 7 da 10 da aka yi masa.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Maina shekaru da dama da suka gabata.
Mai Shari’a ya ce Maina ya saci kuɗaɗen waɗanda ya ce:
“Haƙƙin ‘yan fanshon Najeriya ne, waɗanda yawancin su ma sun mutu ba tare da sun kai ga cin moriyar haƙƙin na su ba.”
Mai Shari’a ya ce ya gamsu da hujjoji da shaidun da masu gabatar da ƙara su ka baje a gaban kotu, waɗanda su ka tabbatar da cewa Maina ya saci maƙudan kuɗaɗen.
“An tabbatar da Maina ya sayi gida kantameme na dala miliyan 1.4 a Abuja.
“Kuma an karya ƙa’ida wajen biyan kuɗin a asirce wuri-na-gugar-wuri, maimakon a biya kuɗin ta banki, kamar yadda doka ta ce duk cinikin da ya haura Naira miliyan 5, to a biya ta banki, ba kuɗi hannu ba.
“An kuma dame shi da kimshe kuɗaɗe a wasu sabbin bankuna biyu, inda ya ɓoye sunan sa, ya ajiye kuɗaɗen da sunan iyalan sa.
“Kuɗaɗen da ya ajiye a bankin sun haɗa da Naira miliyan 300, Naira miliyan 500 da kuma naira biliyan 1.5, waɗanda ya sata daga kuɗaɗen ‘yan fansho.”
Mai Shari’a ya ce Maina ya kasa kare kan sa, sannan kuma gidan da ya saya haƙiƙanin gaskiya ko kusa albashin sa da alawus ɗin sa ko da ya tara su, ba za su iya sayen gidan ba.”