Sojojin Rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ sun bindige Boko Haram ɓangaren ISWAP sama da 50 a wata arangama da su ka sake kafsawa a Ƙaramar Hukumar Askira Uba, Jihar Barno.
Sanarwar da Kakakin Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ta na ɗauke da bayanin cewa a arangamar an kashe manyan kwamandojin ISWAP da ɗimbin dakarun ‘yan ta’addar.
Ya ƙara da cewa an kuma tarwatsa manyan motocin ‘yan ta’adda da dama irin waɗanda nakiya ba ta iya tarwatsa su.
Wannan nasara da aka samu kan Boko Haram, ta zo ne kwanaki uku bayan sojojin Bataliya ta 115 ta yi artabu da ‘yan ta’adda har an kashe Burgediya Janar Dzarma Zirkusu a Askira Uba.
Wannan jarida ta buga labarin Boko Haram sun kashe Janar ɗin sojan Najeriya da wasu sojoji uku.
Mayaƙan Boko Haram ɓangaren ‘yan ISWAP sun kashe Burgediya Janar Dzarma Zirkusu a yankin Ƙaramar Hukumar Askira Uba, cikin Jihar Barno.
Sanarwar da Kakakin Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce an kashe Zirkusu tare da wasu ƙananan sojoji uku, a lokacin da suke kan hanyar kai gudummawar yaƙi ga sojojin da suka jajirce suka hana Boko Haram shiga Askira Uba.
Sanarwar ta yi jimamin rashin mamatan kuma ta ce amma an yi amfani da Sojojin Operation Haɗin Kai, aka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda tare da kashe da dama a cikin su, ta hanyar yin amfani da jirgin yaƙi, manyan motocin yaƙi da manyan bindigogi samfurin Tashi-gari-barde.
Yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da cewa ta na samun nasara kan Boko Haram, a kwanan nan ‘yan Boko Haram sun kai farmaki ba sau ɗaya ba a kan sojoji da wasu farar hula..
Cikin ‘yan shakaru kaɗan da suka wuce ne Kamar Ali ya rasa ran sa yayin da Bataliya sa ke fafatawa da ‘yan ta’adda.
Makonni biyu da suka wuce kuma an nuno Boko Haram sun kama wasu jami’an tsaron ƙasar nan su biyu kuma sun kashe su.
“Sojojin Najeriya sun yi arangama da Boko Haram waɗanda su ka tsere a daidai ƙauyen Leho, cikin Ƙaramar Hukumar Askira Uba, suka kashe da dama tare da lalata motocin yaƙin su.
Sannan kuma sojojin Najeriya sun ƙwato manyan makamai da motocin yaƙi da bindigogi manya a hannun Boko Haram ‘yan ISWAP.
A ranar Asabar ce Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Faruk Yahaya ya jagoranci tawagar manyan sojoji su ka je ta’aziyya ga iyalan marigayi Burgediya Janar Dzarma Zirkusu, kwamandan Bataliya ta 28 da ISWAP su ka kashe.