Bankin Bunƙasa Afrika (AfDB) zai kashe dala miliyan 563 wajen bunƙasa noma da farfaɗo da yankunan karkara a faɗin ƙasar nan.
Daga cikin kuɗaɗen, dala miliyan 110 duk a jihar Kano za a kashe ta.
Shugaban Bankin AfDB Akinwunmi Adesina ne ya bayyana haka a ranar a Asabar a Kano, lokacin da ya je yi wa Aliko Ɗangote ta’aziyyar rasuwar ƙarin sa, Sani Ɗangote.
Shugaban AfDB ya ƙara da cewa za a yi waɗannan gagariman ayyuka a cikin shekarar 2022, inda ayyukan za su ƙunshi bunƙasa noma, aikin gina titina a yankunan karkara, samar da ruwa mai tsafta da kuma inganta tsarin zirga-zirga a yankunan karkara.
Da ya ke ƙarin bayani kan bunƙasa noma, Shugaban AfDB ya ce kuɗaɗen da za a ware za su bunƙasa abinci sosai tare da fito da hanyoyin sarrafa kayan abincin ta yadda masu masana’antu za su rage yawan asarar da su ke yi.
Sannan kuma ya ce wannan tsari na bunƙasa abinci a yankunan karkara zai fitar da al’ummar cikin ƙauyuka daga ƙuncin rayuwa, zuwa wata sabuwar rayuwa mai cike da yalwar albarkar noma.
“Wannan tsari ne na Musamman Don Bunkasa Noma Da Hada-hadar Kayan Abinci, wanda za a fara dasawa a Kano, sannan ya karaɗe faɗin ƙasar nan gaba ɗaya.”
A ɓangaren inganta rayuwar karkara kuwa, ya ce za a gina titina da samar da ruwa mai tsafta a yankunan karkara.
Wannan tsari ne ya ce zai samar da rige-rigen harkokin bunƙasar noma da kasuwancin kayan abinci tun daga karkara har zuwa cikin garuruwa.
Ya ce idan aka bunkadai kayan abinci tare da inganta jin daɗin rayuwar karkara, to za a samu wadata da haɓakar tattalin arziki a cikin al’umma.
Discussion about this post