A daidai hukumar EFCC na ci gaba da binciken Obi Cubana da ya bayyana a gabanta bisa zargin damfara, zamba da sama da fadi da kudaden mutane da suka hada da ta hanyar yanar gizo, sai gashi kuma babban dan shugaban hukumar tsaro na sirri, Yusuf Bici na caccakar hukumar kan aikinta.
Abba Bichi wanda kwararren dan kwallon kafa ne, ya ce Obi Cubana mutumin kirki ne abin koyi ga kowa.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan labari, Abba bai cire wannan zargi nasa a shafin sa ta instagram ba.
” EFCC na muzguna wa matasa da ke cin gumin amma sai su rika kafa musu kahon zuka haka kawai.
Discussion about this post