Gwamnatin Inuwa Yahaya ta bayyana cewa ba za ta kyale wani a jihar ya rika zuwa yana tada zaune tsaye ba, kuma gwamnati ta kau da ido.
Wannan kalamai na kunshe ne a jawabin da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Julius Ishaya, ya yi bayan hari da wasu ‘yan takife suka kaiwa tsohon gwamnan jihar Danjuma Goje a garin Gomne ranar Juma’a.
Ishaya ya ce gwamnati ba zata suba wa koma waye ido ba, komai matsayin sa ya rika shigowa gari yana neman tada zaune tsaye ba.
Gwamnatin Gombe ta ce rikici ne ya barke tsakanin gungun ‘yan daban da ke yi wa Goje rakiya daga filin jirgin saman Gombe suka rika sarar juna. Daga nan ne gwamnati ta tura jami’an tsaro domin kada abin ya wuce gona da iri.
Amma kuma daga bangaren tsohon gwamna Sanata Goje, kakakin sa ta shaida cewa da gangar hadiman gwamnan suka datse hanyar shiga gari da suka tabbatar sanata Goje na zuwa. Wanna daliline ya sa rikici ya barke har mutum daya ya rasa ransa bayan an farfasa wa sanatan motocinsa.
A yammacin Asabar kuma diyar Goje, Hussaina ta mika wa gwamnati Inuwa Yahaya takardar sauka daga mukamin kwamishina a gwamnatin sa.
Sai dai kuma masu yin fashin baki sun ce murabus din da ta yi na da nasaba da rashin jituwa tsakanin mahaifin ta da gwamnan jihar Yobe