Hukumar Kula da Ɓarnar Mai ta Ƙasa (NOSDRA) ta bayyana cewa tsawon kwanaki 10 kenan mai na malala a ƙasa, a Nembe, yankin Neja Delta, amma ba a magance malalar man ba.
An ce man ya na fita ne tun daga ranar 5 Ga Nuwamba daga wata rijiyar ɗanyen mai da ke cikin kadada mai Lamba OML 29, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Jamii NOSDRA sun je domin haƙiƙance irin ɓarnar da aka yi da kuma gano musabbabin malalar ɗanyen fetur ɗin, amma sun kasa, saboda man da ke malala ya hana su gudanar da binciken komai.
Daraktan NOSDRA, Idris Musa, ya shaida wa manema labarai cewa an kasa toshe inda danyen man ke fitar har zuwa ranar Lahadi.
Idris ya ƙasa da cewa irin yawan man da ya malale a ƙasa ya sa kan kasa tantance dalilin malalewar da kuma samun damar yin bincike.
An tambaye shi ko an toshe inda danyen mai ke zuba? Idris ya ce har yau ɗin nan ba a kai ga toshewa ba.
“Amma an kirawo wani kamfani mai saurin kwashe dagwalon ɓarnar danyen mai, domin ya gaggauta gyara wurin..
“Mun fara da yin wannan domin magance wata barna ta kusa ko ta nesa da man zai haifar a cikin yankin.” Inji Idris Musa.
Ya ce tilas sai an nemi agajin ƙasashen waje domin kamfanin Aiteo Eastern Exploration Company ya kasa shawo kan matsalar.
Filin haƙo ɗanyen mai mai lamba OML 29, ya na ɗauke da rijiyoyi na mai 11, kuma ya na haƙo ganga 600,000 a kullum.
Kamfanin Aiteo ya sayi filin cikin 2015 a hannun Shell Development Company, kan kuɗi dala biliyan 1.7.
Discussion about this post