Cikin wannan makon labarin da PRNigeria ta buga ya karaɗe ƙasar nan da sanarwar mutuwar Dogo Giɗe, kuntukurmin ɗan bindigar nan maras imani a zuciya, kuma maƙetaci.
Jaridu sun cika da labarin mutuwar Dogo Giɗe, wanda PRNigeria ta ce wani ɗan bindiga ya bindige shi.
To sai dai kuma har yanzu babu sani tartibin sahihin bayanin lallai an kashe Dogo Giɗe ɗin har yanzu.
Dogo Giɗe, wanda shugaban wani gungun ‘yan bindiga ne marasa imani, masu yin kisa, banka wa ƙauyuka wuta, garkuwa da mutane, satar shanu, lalata da mata da kwasar abinci, sun tanadi muggan makamai.
Sunan sa na yanka Abubakar Abdullahi, wanda a cikin dazukan Karu aka haife shi.
Ya kafa sansanin sa a cikin Dajin Kuyanbana a Zamfara, inda daga can ya ke kai hare-hare a jihohin da su ka yi maƙautaka da sansanin na sa, irin su Kaduna, Kebbi, Neja da cikin Zamfara ɗin.
Muggan bindigogin da Dogo Giɗe ya tanada ne ya kai shi ga ƙulla alaƙa da Boko Haram da su ISWAP.
A cikin 2018 ne ya kashe ogan sa Buharin Daji, kuma kwanan nan ya kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga maras imani, mai suna Damina.
Fitaccen malamin tarihin Jami’ar Danfodiyo ta Sokoto, Farfesa Mukhtar Ahmed-Rufai, ya ce labarin kisan Dogo Giɗe ba gaskiya ba ne.
“Kawai duk farfaganda ce sojoji ke yi kawai.” Inji shi.
Tsohon ma’aikacin jaridar HumAngle Yusuf Anka shi ma ya ce ya bi duk majiyar da zai iya bi, amma ana tabbatar masa cewa Dogo Giɗe bai mutu ba.
“Ko a ranar Juma’a a garin Babbar Doka Dogo Giɗe ya yi Sallar Juma’a. Kuma tun da safe ya shiga garin, bai fita ba sai ƙarfe 6 na yamma.
“A ranar Lahadi ɗin nan ma Dogo Giɗe ya shiga garin Babbar Kuka har ƙarfe 1 na yamma.” Inji Yusuf Anka.
Shi kuma Basharu Guyawa, Shugaban Ƙungiyar Rundunar Adalci a Sokoto, ya ce batun mutuwa ko kisan Dogo Giɗe ba gaskiya ba ce.
“Da Dogo Giɗe ya mutu ko an kashe shi, za mu yi matuƙar murna sosai. Amma dai a yanzu labarin ya na nan da ran sa, ya fi labarin kisan sa ƙarfin inganci da sahihanci.”
Dogo Giɗe shi da yaran sa ne su ka kwashe ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri, a Jihar Kebbi, a cikin watan Yuni.
Discussion about this post