A ranar Litinin ne shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Ibrahim Gambari ya dasa tubalin ginin asibitin kula da shugaban ƙasa da manyan hadiman gwamnati.
A taron wanda manyan hadiman gwamnati suka halarta Gambari ya ce asibitin bayan an kammala shi zai rika kula da lafiyar shugaban ƙasa da iyalen sa, mataimakin shugaban ƙasa da iyalan sa sannan da bakin shugabannin wasu kasashen idan su zo ziyara Najeriya kuma bukatar ganin likita ya tasa.
Ya ce za a kammala ginin asibitin a watan Disembar 2022.
Idan ba a manta ba a watan Oktobar 2017 PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta bakin cikinta da koke-koken matsalolin rashin kudi da asibitin da ke fadar shugaban kasa ke kukan yana fama da shi.
Ta ce abin kunya ne irin kukan da asibitin ke yi na rashin kayan aiki da hatta maganin ciwon kai ‘Panadol’ wai babu a asibitin bayan naira biliyan 3 da gwamanti ta ware wa asibitin.
Ta ce ta ji labarin halin da asibitin ke ciki ne wani lokaci da bata da lafiya.
Discussion about this post