A gidan mutuwa ne kaɗai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta iya jefa ƙafa ta ciwo bashi domin tafiyar da gwamnati.
Har yanzu akwai ɗimbin ayyukan da a takarda kawai su ke, da kuma tulin buhunan alƙawurran da Buhari ya yi, amma bai cika ba, saboda rashin kuɗaɗe.
Sai dai kuma abu ɗaya da Gwamnatin Buhari ba za ta iya yi domin samun kuɗaɗen gudanar da ayyuka ba, shi ne rage kashe kuɗaɗen tafiyar da ayyukan gwamnati na yau da kullum.
Yayin da a duk shekara ake fama da wawakeken giɓin kasafin kuɗi, ko a na 2022 an samu giɓin da sai an ciwo bashin sama da naira tiriliyan 5.
Gwamnatin Buhari ta gwammace ta yi ta ɗirka wa cikin ta da cikin ‘yan Najeriya bashi, maimakon ta rage kashe kuɗaɗe a ɓangarorin da kashe kuɗaɗen ba su da wata fa’ida, tasiri, alfanu ko wata riba mai muhimmanci, sai ma ɗibga asara da ake yi.
Wanda ya fi amfana da wannan almubazzarantar da kuɗaɗen Najeriya shi ne Muhammadu Buhari da kan sa.
Yayin da a kullum ba shi da wata magana sai tsantsenin a daina kashe kuɗaɗen bakatatan, amma kuma a duk shekara kasafin sa musamman na abinci da sauran fannonin rayuwa, sai ƙaruwa ya ke yi har ta kai ga ya na nunkawa.
Kasafin 2022: Buhari Zai Sai Wa Ofishin Sa Motocin Naira Biliyan 1.6.
Dama kuma a shekarar 2021 Buhari ya sai wa ofishin sa sabbin motoci na Naira miliyan 500.
A shekaru shida da Buhari ya shafe a ofis, ya sai wa ofishin sa motoci na Naira biliyan 5.
Waɗannan motoci kuɗin su zai isa a gina asibitocin kula da marasa lafiya 500 a kan Naira miliyan 10 kowane.
Ofishin Buhari ya na ta ƙara kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen abinci, sutura, tafiye-tafiye, asibitin shugaban ƙasa da kuma ɗimbin kuɗaɗe wajen kula da bargar jiragen Shugaban Ƙasa, waɗanda kafin ya hau mulki ya yi alƙawarin sayar da su domin Najeriya ta samu kuɗi.
Hausawa sun ce kamar Kumbo kamar kayan ta. Yadda Buhari ke facaka da kuɗaɗen al’umma wajen inganta tafiyar da rayuwar sa, haka su ma Gwamnonin Najeriya ke irin wannan rayuwar ta fifita kashe kuɗaɗe wajen inganta ta su rayuwar.
Kasafin Abincin Buhari: Yadda Buhari Ya Nunka Kasafin Abincin Sa Na 2022, Ya Bar Talakawa Da Gaganiyar Neman Kuɗin Sayen Garin Masara:
Matsalar ƙuncin rayuwa da tsadar kayan abinci a Najeriya ba ta buƙatar dogon bincike. Babban ma’aunin gane irin halin ƙuncin da talakan Najeriya ke ciki, shi ne nazarin kasafin abincin da Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo za su lashe cikin 2022.
Kuɗaɗen da Shugaba Buhari ya ware domin sayen kayan abinci a shekarar 2022, sun nunka na 2021, sun ruɓanya na 2019, 2018. Domin na waɗannan shekaru duk ba su wuce duk shekara abincin Naira miliyan 195.5 ba.
Amma a kasafin 2022, Buhari da Osinbajo za su ci abincin Naira miliyan 457. Kun ga neman bayan sun nunka, har ma sun haura da kusan Naira miliyan 56.
Buhari ya ƙara wa kan sa da Osinbajo kuɗin sayen kayan abinci, saboda tashin farashin kayan abinci da kayan masarufi.
Ya yi wannan ƙari a lokacin da gwamnatin sa ke kukan ƙarancin kuɗaɗe, tare da yawan ciwo basussuka a ƙasashen ƙetare.
Sai dai kuma tun daga watan Maris, 2021, lokacin da farashin kayan abinci ya yi tashin da shekaru 12 a baya bai yi irin sa ba, talakawa su ka shiga cikin wani halin gaganiyar neman abin sakawa a bakin salati.
Rufe kan iyakoki ya ƙara hasala tsadar kayan abinci, ta kai yanzu talakawa shinkafar cikin gida ma na neman gagarar su, da yawa sun koma sayen niƙaƙƙen garin masara domin yin tuwo.
A lura da yadda kayan abinci ke kara tsawwala tsada. A cikin 2017 Buhari ya yi kasafin abincin Naira miliyan 115 shi da mataimakin sa. Amma a cikin 2022 zai cinye abincin Naira miliyan 301 shi kaɗai. Sai matakimakin sa na Naira miliyan 156.