Tsohon Sanatan Zamfara Kabiru Marafa, ya bayyana cewa barazanar za a kore shi daga APC zancen shirme ne, kuma shi ba ƙaramin ƙwaron da jam’iyyar APC za ta iya yi wa barazana ba ce.
Ya ce korar sa idan ma an yi daga APC, ba shi ne zai magance matsalar ba, sai ma hakan ya ƙara rura tashin wata wutar mai ƙarfi fiye da ta yanzu.
A ranar Lahadi ne Marafa ya ce Gwamna Mala Buni bai cancanci riƙe APC ba, tunda a gefe ɗaya ya na riƙe da kujerar gwamnan Jihar Yobe.
Marafa ya sha alwashin maka Kwamitin Shirya Taron Gangamin APC a kotu, domin a cewar sa, kwamitin haramtacce ne, domin haramtaccen shugabancin Mala Buni ya kafa kwamitin.
An naɗa Kwamitin Tafiyar da APC cikin 2020, a ƙarƙashin Mala Buni, cikin 2020, bayan jam’iyyar ta wancakalar da Adams Oshiomhole.
“Kwamitin Mai Mala Buni haramtacce ne. Ba zai iya shirya wani taron komai ba ko zaɓen fidda gwani ko wani abu a bisa doka.
“Zan ƙalubalance shi a kotu, kuma ban damu da duk abin da wani zai faɗa ba, ya je ya faɗi. Buni ya tsokane ni, kuma zan nuna masa cewa dodo ya tsokana. Ya zungure ni sau ɗaya, ni kuma sai na zungure shi sau goma.
” Duk wani abin da Buni ya yi wa APC tun daga hawan sa, haramtacce ne. Zan maka shi kotu. Mafi alheri ga APC shi ne ta tsige Buni daga shugabanci, kafin ya gurgunta jam’iyya ta kasa ko da rarrafe, ballantana gudun tsere.” Haka Marafa ya bayyana a ranar Lahadi.
A kan haka ne jam’iyyar APC ta yi barazanar korar Sanata Marafa, bisa zargin sa da rashin ɗa’a da yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.
Marafa ya nusasshe da uwar jam’iyyar APC cewa: “Sashe na 17(4) na Dokar Najeriya ya haramta duk wani mai riƙe da muƙamin shugabancin jam’iyya a riƙe muƙamin mulkin jama’a a lokaci ɗaya.”
A nan ya na nufin Gwamna Mala Buni tunda ya na riƙe da muƙamin mulkin jihar Yobe, to doka ta haramta masa karɓar muƙami a cikin shugabancin jam’iyya.
Ba Sanata Marafa ne kaɗai ya fara bayyana wannan matsayar ba, da dama sun gargaɗi APC a kan matsalar damƙa shugabanci a hannun Buni, inda su ka ce kotu na iya soke duk wani ɗan APC da ya yi nasarar cin zaɓe a lokacin shugabancin Buni, tun daga kansila har shugaban ƙasa.
Discussion about this post