Kamfanin Simintin Ɗangote ya sayar da siminti tan miliyan 22.2 a cikin watanni 9.
Cikin wata sanarwar da Dangote Cement ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an samu cinikin naira tiriliyan 1 da biliyan 200 a cikin waɗannan watanni 9 ɗin tsakanin watan Janairu zuwa Satumba.
Cinikin da aka samu tsakanin wadannan watanni 9, ya haura wanda aka samu a watanni 9 na shekarar 2020 da kusan kashi 34% bisa 100%.
An danganta ƙarancin cinikin a 2020 da ɓarkewar cutar korona. Kuma an danganta ƙaruwar ciniki a wannan shekarar da yawan gine-ginen da ake yi a cikin 2021.
Shugaban Kamfanin Dangote Cement, Aliko Ɗangote ke da kashi 85.9 na ilahirin jarin masana’antar.
A yanzu dai duk buhu ɗaya mai nauyin kilogiram 50, ana sayar da shi a kan Naira 3,400.
A cikin wannan ciniki na Naira tiriliyan 1.2, Dangote ya samu ribar Naira biliyan 403.5 kafin a ware kuɗaɗen haraji.
Amma idan aka ware harajin gwamnati, zai tashi da Naira biliyan 278.8.
Cikin makon shekaranjiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa MTN ya yi cinikin Naira Tiriliyan daya a Najeriya a cikin watanni 9 na Janairu zuwa Satumba.