Kungiyar ‘yan Arewa mazauna yankin kudu maso gabashin kasar nan wato yankin kabilar Igbo ta yi kira ga ƴan Najeriya da su baiwa ƴan kabilar dama wanin su ya shugabanci Najeriya a 2023.
Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Umaru, ya yi wannan roko ne a taron manema labarai ranar Lahadi a garin Umuahia.
Umaru ya ce a cikin manyan ƙabilun ƙasar nan ƴan ƙabilar Igbo ne ba su nuna banbanci da kyamar bako, sun rungumi kowa a matsayin nasu ne.
” Roko na shine a ci gaba da samun haɗin kai a tsakanin mutanen kasar nan, sannan kuma ina yin kira ga ƴan Najeriya su taru wuri guda a haɗa kai gaba ɗaya a mara wa ɗan ƙabilar Igbo baya ya shugabanci ƙasar nan a 2023.
” Yanki Arewa, da sauran yankunan kasar nan duk sun yi mulki banda Inyamiri, Wannan shine lokacin da ya kamata mu haɗu kaf ɗin mu mu baiwa ɗan yankin haɗin kai mu zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.
“Idan muka ba su goyan baya suka yi shugabancin kasar nan Kuma ya yi kyau za mu iya ba su dama si yi tazarce a karo ta biyu.
“Mu duka mutanen Arewa mazauna yankin kudu maso gaba muna goyon bayan su kuma su za mu mara wa baya su shugabanci Najeriya.
A karshe Umaru yayi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar siyasar yankin da su haɗa hannu su zabo ɗan takara nagari wanda zai iya kaiwa ga nasara.
” Muma a namu ɓangaren mun fara tuntubar juna game da tsara irin gudunmawar da za mu bada don su kai ga cimma wannan buri na su.