Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Enugu ta damƙe wani magidanci mai suna Anyishi Chidi kan zargin ya kashe ɗan sa, da nufi yin tsafi don ya samu kuɗaɗe.
Kakakin Yaɗa Labarai na Jami’an Tsaro na Enugu, Daniel Ndukwe ne ya sanar da haka a wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Alhamis.
Ndukwe ya ce an kuma kama wani fasto wanda makaho ne, bisa zargin sa da hannu wajen kisan yaron domin uban yaron ya samu kuɗin tsafi.
Ndukwe ya ce tun da farko dai an nemi yaron ba a gani ba, a ranar 22 Ga Oktoba. Amma daga baya sai aka gano kashe yaron aka yi ta hanyar tsafi.
Yaron ɗan shekara 7 a haihuwa, mahaifin na sa kuma shekarun sa 36.
“Yayin da aka sanar wa jami’an ‘yan sanda ɓatana yaron, sun damƙe mahaifin sa a ranar 6 Ga Nuwamba, inda bayan ya sha tambayoyi, ya amsa laifin zargi sa da ake yi da kisan ɗan na sa.
“Ya kuma kai mu inda muka kama wani makahon dattijo mai shekaru 95, wanda kuma fasto ne, bayan an tabbatar da hannun sa wajen yin tsafi da yaron.
“Daga nan mahaifin yaro ya kai jami’an tsaro har wajen wata ƙarama, inda ya gina rami maras zurfi ya rufe gawar yaron.”
Yan sanda dai sun tono gawar yaron bayan ta rigaya ta ruɓe.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Enugu, Lawal Abubakar, ya ja kunnen a riƙa kula da ƙananan yara sosai.