Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun karfe 1 na daren Talata ne wasu ƴan bindiga suka dira jami’ar Abuja inda suka sace wani farfesa da ƴaƴan sa biyu.
Farfeasan mai suna Obansa Joseph yana karantarwa ne a sashen koyar da Tsimi da Tattali wato Economics a jami’ar.
Bayan shi da suka sace sun yi awon gaba da ƴaƴan sa biyu wanda ba a bayyana sunayen su ba.
Haka kuma mahukuntan jami’ar sun bayyana cewa ƴan bindigan sun sace wasu ma’aikatan jami’ar wanda ba malamai bane 6, duk sun yi awon gaba da su.
Jami’in Hulɗa da Jam’a na jami’ar, Habib Yakoob, ya bayyana cewa tuni an sanar da jami’an tsaro kuma sun fantsama farautar ƴan bindigan.