Aƙalla ƴan Najeriya fiye da miliyan 1 ne suka zama ‘yan gudun hijira a cikin watanni 12. Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ce ta bayyana haka.
Kwamishinar Tarayya ta Hukumar NCFRMI, Imaan Sulieman-Ibrahim ta bayyana haka, a lokacin da ta ke kare kasafin hukumar na 2022 a gaban kwamitin Majalisar Tarayya, a ranar Litinin a Abuja.
Ta ƙara da cewa aƙalla akwai Ƴan Najeriya miliyan 3 da a yanzu haka ke zaune a sansanin masu gudun hijira daban-daban.
Imaan ta ƙara da cewa akwai masu gudun hijira cikin Najeriya har mutum 73,000 daga ƙasashe 23.
Sannan kuma akwai Ƴan Najeriya sama da 500,000 da ke gudun hijira cikin ƙasashen Chad, Nijar, Kamaru, Mali, Libiya da sauran ƙasashe.
Imaan ta ce hukumar na ƙoƙarin gina wani gari sukutum da masu gudun hijira za su riƙa zama a matsayin muhalli a Barno, Kano, Edo da Katsina.
Imaan ta ce a gaskiya kasafin hukumar ya yi kaɗan matuƙa, ta yadda ko kashi 5 cikin 100 na buƙatun hukumar ba sa su iya magancewa ba.p