Babban malamin nan na Kaduna kuma wanda ya riƙa kurɗa-kurɗar shiga wurin ‘yan bindiga, Sheikh Ahmed Gumi, ya gargaɗi Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya cewa kada su ayyana sunan ‘yan bindiga su ce musu ‘yan ta’adda.
Duk da kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ‘yan bindiga ke yi, Gumi ya ce za a yi da-na-sani idan aka yi amfani da dokar ƙasa aka kira su ‘yan ta’adda.
Gumi wanda tsohon soja ne, kuma likita, ya daɗe ya na kamfen ɗin neman a yi wa Fulani ‘yan bindiga afuwa.
Ya shiga wurin ‘yan bindiga a dazukan Kaduna, Neja, Katsina, Sokoto da Zamfara. Kuma ya je jihohin inda ya gana da gwamnoni da gaggan gogarman ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane, da nufin a samu maslahar magance matsalolin da ke addabar yankunan.
Ko kwanan nan Gwamnan Katsina da na Kaduna sun nemi a bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne, domin sojoji su samu cikakkiyar damar murƙushe su.
Sai dai Gumi a cikin wani bayani da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya yi babban kuskure ne idan aka bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.
Duk da ya nuna cewa su ma ‘yan bindiga su na kisa da ɓarnatar da dukiyar jama’a da garkuwa da mutane, to amma siyasa ta shiga cikin zukatan jama’a, musamman masu cewa su ma ‘yan bindiga ai ‘yan ta’adda ne.
Ya yi tsokaci kan yadda ‘yan bijilante ke kashe Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba, su ce duk ‘yan bindiga ne, abin da Gumi ya ce hakan kan tunzira sauran su shiga ƙauyuka kisan ramuwar-gayya.
Gumi ya bayyana irin ƙoƙarin da ya yi har ya sa wasu Fulani ‘yan bindiga masu yawa su ka tuba, su ka daina.
“Sai dai abin takaici, ba ni da masu taya ni wannan mawuyacin aiki da nake yi, maimakon haka ma, sai tulin masu gaba da ni na ke ƙara samu a kullum.”
Ya yi fatan a samu wani limamin Kirista na Igbo da ka Yarabawa su je su lallashi Nnamdi Kanu da su Sunday Igboho masu son ɓallewa daga Najeriya.
Ya ce idan su ka wayar wa magoya bayan su kai, za a samu maslahar zamantakewa tare da juna a matsayin mu na ƙabila daban-daban masu zaune a ƙasa ɗaya.
Ya ce malaman addini za su iya taka muhimmiyar rawa inda tsarin da babu addini ba zai iya yin tasiri ba.
Sai dai ya nuna takaicin maimakon jama’a su tashi tsaye a kwantar da wannan mummunar fitina, sai kowa ya yi zaman sa cikin ɗaki. Ya dararrashe ya na ta watsa bayanai barkatai waɗanda ba za su taɓa zama mabuɗin kawo ƙarshen fitintinu ba.
A ranar Lahadi ce dai Buhari ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ba su da bambanci da Boko Haram.
Duk da dai har yau Shugaba Buhari bai fito ya bayyana ‘yan bindiga cewa su ma ‘yan ta’adda ne kamar yadda ake kiran ‘yan Boko Haram ba, a ranar Lahadi ya bayyana cewa “a wani ɓangaren ‘yan bindiga ba su da wani bambanci da ‘yan Boko Haram.”
Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka, a ranar Lahadi, bayan da wata mujalla mai suna The Economist, wadda ake bugawa a Landan ta buga labari cewa rashin tsaro a Najeriya ya ƙara dagulewa a ƙarƙashin mulkin Buhari.
‘Yan bindigar dai yanzu sun yi ƙarfin da har sun kai ga harbo jirgin yaƙin Najeriya ɗaya. Waɗanda Shehu ya ce sun yi ƙarfin tara kuɗaɗe da muggan makamai. “Kenan a nan ba su da wani bambanci ma da Boko Haram, waɗanda su a yanzu ma an yi masu tara-tara, an matse su a wuri ɗaya.”
‘Yan Najeriya da dama ciki har da Majalisar Dattawa da Gwamna El-Rufai na Kaduna, duk sun yi kira ga Buhari ya kira ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.
A martanin da Shehu ya yi masu, ya amince akwai ƙalubale daban-daban kan matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan daban-daban.
Sai dai kuma ya ce duk Shugaba Buhari ya na ta ƙoƙarin magance matsalolin.
“Mujallar The Economist ta yi gaskiya, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da dama. Sai dai a lura ba a cikin wannan gwamnatin matsalolin su ka faru ba. Wannan gwamnatin ce ma ke ta ƙoƙarin magance waɗannan ɗimbin matsalolin. “Alhali gwamnatocin baya babu wadda ta yi ƙoƙarin magance ko da matsala guda tal.” Inji Garba Shehu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Ko a cikin makon da ya gabata, sai da Gwamna El-Rufai ya goyi bayan Majalisar Dattawa Tarayya domin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda.
Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana goyon bayan sa ga Majalisar Tarayya, wadda ta yi kira ga Gwmnatin Tarayya cewa ta shaida wa duniya ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne kawai.
El-Rufai ya ce idan aka bayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne, to hakan zai ƙara zaburar da sojoji su darkake su a duk inda su ke, su na yi masu kisan kan-mai-uwa-da-wabi, ba tare da tsoron ƙorafe-ƙorafe daga bakunan ƙungiyi kare haƙƙi na kasashen duniya ba.
Gwamnan ya yi wannan furucin a ranar Laraba, a Kaduna, lokacin gabatar da Rahoton Matsalolin Tsaro Na Watanni Uku na kusa da ƙarshen shekara.
An gudanar da taron a Gidan Sa Kashim na Kaduna.
Ya na magana ne a kan ɓarnar da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi a jihohin Arewa maso Kudu, ciki kuwa har da jihar Kaduna.
“Mu dama a jihar Kaduna mun daɗe da nuna goyon bayan a kira ‘yan bindiga da sunan ‘yan ta’adda kawai. Cikin shekarar 2017 mun rubuta wa Gwamnatin Tarayya wasiƙa mu ka nemi ta bayyana cewa ɗan bindiga fa ɗan ta’adda ne.
“Saboda sai fa an gwamnatin tarayya ya kira su da suna ‘yan ta’adda, sannan sojoji za su samu ƙarfin da za su riƙa yin shigar-kutse a cikin dazuka, su na yi masu kisan-kiyashi, yadda ƙungiyoyin ƙasashen waje ba za su riƙa yin matsin- lamba ga Sojojin Najeriya ba. Kuma ba za a ce Sojojin Najeriya sun karya dokar ƙasa-da-ƙasa ta ba.
“Don haka mu na goyon bayan matsayar da Majalisar Tarayya ta cimma, inda za mu ƙara aika wa Gwamnatin Tarayya cewa Jihar Kaduna na goyon bayan raɗa wa ‘yan bindiga sabon suna ‘yan ta’adda.
“Yin haka ne zai ba sojoji ƙarfin guiwar tashi tsaye haiƙan su murƙushe su, ba tare da wata tsugune-tashi ta biyo baya ba.”
El-Rufai ya nuna damuwa dangane da yadda a kullum ake samun rahotannin hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna, duk kuwa da irin maƙudan kuɗaɗen da jihar ke kashewa wajen samar da tsaro ga jami’an tsaro a jihar.
“Ina mai takaicin ganin yadda duk da ɗimbin kuɗaɗen da muke kashewa a ɓangaren tsaro, amma a ce har yanzu babu wata alamar raguwar hare-haren da ake kai wa jama’a a jihar.”
Daga nan sai ya roƙi gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 774,000, wato a ɗauki 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma, domin ayyukan inganta tsaro a Najeriya.