Gabatowar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, babban limamin Ɗariƙar Katoliƙa na Ekiti a Jihar Ekiti, Bishof Felix Ajakaye, ya hori ‘yan Najeriya su zaɓi shugaba wanda ya ke lafiyayye garau, kuma wanda ya cancanta zai iya samar wa ƙasar nan ci gaban da ta ke buƙata.
Ajakaye ya yi tsokaci cewa yayin da ake ta ƙara ƙarfafa tsarin karɓa-karɓa, to ko daga ina shugaba zai fito dai ya kasance “an zaɓi wanda ya cancanta, mai lafiya kuma managarcin mai kaifin ƙwaƙwalwa.”
Bishof ɗin ya yi wannan magana a Ado Ekiti babban birnin jihar, a lokacin da ya ke jawabi a wurin wani taro.
Limamin babban cocin ya karanta takarda ce mai magana kan muhimmancin shugabanci nagari, a taron shekara-shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Ekiti, Reshen Wakilan Jaridu na Ƙasa.
An gudanar da taron a Ɗakin Taro na otal ɗin Prosperous Royal Hotels and Resort Centre.
Ajakaye ya ce wajibin al’ummar kowace jiha ce su zaɓi mutanen kirki a matsayin gwamnonin da za su iya samar masu bunƙasar tattalin arziki, kuma su iya kawo karshen kashe-kashe, ta’addaci da aika-aikar ‘yan bindiga.
“Mu na buƙatar ‘yan Najeriya masu himma da ƙwazon kishi kuma wanda ya cancanta a matsayin shugaban ƙasa, gwamna kafin mu kai a inda mu ke fatan mu kai.”
Bishof Ajakaye dai bai bayyana sunan ko da shugaban ƙasa da ya a baya da ya yi fama da rashin lafiya.
“Kamata ya yi duk wani mai neman zama shugaba a Najeriya, ya kasance lafiyayye ne garau, a lafiyar jiki da lafiyar tunani.
“Mun gaji da talasurun shugaban da ba ya iya taɓuka komai, sai dai amfani da ƙarfin fadawan sa kawai.
“Mu daina bari ‘yan-amshin-Shata da ‘yan zaman fada na jan akalar ƙasar mu. Idan mu ka ci gaba da zama a haka, to mu na cikin gagarimar matsala fa.”
Yayin da Shugaba Umaru ‘Yar’Adua ya sha fama da rashin lafiya har ya mutu a kan mulki, shi kuwa shugaba Buhari ya sha fama da zama jiyya da jeƙala-jeƙalar zuwa Landan ganin likitocin sa.
Discussion about this post