Ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Zango na jam’iyyar PDP Francis Zimbo ne yayi nasara a zaɓen ƙaramar hukumar Zangon Kataf da aka yi ranar Asabar.
Idan ba a manta ba hukumar zaɓe ta jihar Kaduna ta ɗage zaɓukan ƙananan hukumomin Zangon Kataf da na Birnin Gwari zuwa ranar Asabar saboda matsalar tsaro.
Malamin zaɓe Nuhu Garba ya bayyana cewa Zimbo na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 28,771 shi kuma John Hassan na jam’iyyar APC, ya sami kuri’u 19,509.
Sannan kuma PDP ce ta lashe kujerun Kansiloli 9 cikin 11 da dake karamar hukumar.
Discussion about this post