Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Anambra a ranar 6 ga Nuwamba zai ba maraɗa kunya wajen tsare gaskiya domin kuwa ta samar da dukkan kayan aiki da za su taimaka wajen tabbatar da aikin zaɓen a cikin nasara.
Kwamishinan Zaɓe na INEC a Jihar Anambra (REC), Dakta Nwachukwu Orji, shi ne ya bayyana haka a garin Awka, a lokacin da aka yi wani taron ilmantarwa tare da faɗakar da masu zaɓe naƙasassu da kuma ƙungiyoyin mata.
An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar wata gidauniyar tsara zaɓuɓɓuka ta ƙasar Amurka mai suna ‘International Foundation for Electoral Systems’ (IFES), da Cibiyar Tallafin Cigaban Ƙasashe ta Amurka (United States Agency for International Development, USAID) da wata ƙungiyar inganta tsarin zaɓe da na siyasa mai suna ‘Consortium for Elections and Political Process Strengthening’.
Orji, wanda shugaban sashen ilmantarwa da faɗakar da masu zaɓe na INEC a jihar, Mista Samuel Nimem, ya wakilta, ya ce hukumar ta kammala kusan dukkan wani tanadi da ya kamata don gudanar da zaɓen.
A cewar sa, wannan zaɓe zai ƙaryata duk wani tunani da wasu ke yi na cewa wai INEC ta na yin maguɗi ko ta na aikata almundahana a zaɓe.
Ya ce, “INEC ta gama shiri a kowane mataki na yin wannan zaɓe. Kayan zaɓe da su ka ƙone kwanan nan lokacin da aka kawo mana wani hari duk an musanya su, kayan aiki marasa hatsari duk an rarraba su a dukkan yankunan ƙananan hukumomi, kuma ana gudanar da horas da jami’ai da ma’aikatan wucin-gadi yanzu haka da na ke magana da ku.
“Mun liƙa rajistar masu zaɓe tare da miƙa ta ga jam’iyyun siyasa da su ka shigar da ‘yan takara, mun wallafa jerin sunaye na ƙarshe na ‘yan takara, sannan mu na ci gaba da haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da tsaro a dukkan cibiyoyin zaɓe.
“Mun ƙara yawan cibiyoyin zaɓe zuwa 5,720 don bada dama ga masu zaɓe su kaɗa ƙuri’ar su, kuma mu na gudanar da aikin ilmantarwa da faɗakar da masu zaɓe gadan-gadan tare da yin kira ga jama’a da su je su aiwatar da haƙƙin su na ‘yan ƙasa.
“Da yake mun tanadar da dukkan kayan aiki sannan za a aika da sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura, ina faɗa maku cewa zaɓen Anambra zai ba maraɗa kunya wajen tsare gaskiya. Hakan zai ƙarfafa ran mutane game da tsarin mu na zaɓe.”
Orji ya yi kira ga naƙasassu da su fito su taka rawa a kowane mataki na harkar zaɓe domin hukumar ta tanadar da wadatattun tsare-tsare wajen taimaka masu su jefa ƙuri’a.
Ya ce, “Naƙasassu muhimman ‘yan ƙasa ne, saboda haka mu na ba su kula ta musamman ta hanyar samar da yanayin da za a yi komai tare da su.
“Wajibi ne ku shiga harkar zaɓe sosai da sosai saboda dukkan ku ‘yan Nijeriya ne kuma ku na da ‘yancin ku yi zaɓe kuma a zaɓe ku. Ina tabbatar maku da cewa mu na yin dukkan abin da za mu iya yi don tabbatar da tsaron lafiyar ku.”
Orji ya yi kira ga jama’a da kada su riƙa nuna halin ko oho game da al’amuran zaɓe, ya ce dama ce mutum ya samu ta zaɓen ɗan takarar da ya ke so.
Ita ma a nata jawabin, Hajiya Amina Yahaya, wadda ta zo daga IFES, ta ce ƙungiyar su ta sadaukar da kan ta wajen duk wata hanya da za a bi a inganta rayuwar naƙasassu da mata.
Ta ce, “Mu na goyon bayan wannan shiri saboda mu na so duk wani gungun marasa ƙarfi a riƙa tafiya tare da su a harkar zaɓe saboda su na da ‘yancin su zaɓi shugaban da su ke so.”
A nata jawabin ita ma, Misis Dorothy Bello, Mataimakiyar Darakta ta ƙungiyar ‘Civil Society Organisation’, ta ce mata da naƙasassu muhimman masu ruwa da tsaki ne waɗanda bai kamata a yi watsi da su ba a lokutan zaɓe.
Ta ce, “Aikin da ya rataya a wuyan INEC shi ne ta shirya zaɓe fisabilillahi ba tare da nuna wariya ga kowa ba; kuma naƙasassu da mata su na buƙatar su aiwatar da ‘yancin su na su zaɓa kuma a zaɓe su ba tare da nuna bambanci ba.
“An shirya wannan taro ne domin a faɗa maku cewa INEC ta na samar da kyakkyawan yanayi ga kowa da kowa, ba tare da kula da matsayin ka ba. An yi wannan tsari domin a ilmantar da ku dangane da yadda za ku aiwatar da ‘yancin ku na yin zaɓe ba tare da wani shamaki ba.”
A yayin da ya ke yaba wa INEC saboda hoɓɓasan da su ke yi ya zuwa yanzu, Mista Ugochukwu Okeke, Shugaban Haɗakar Ƙungiyar Naƙasassu ta Ƙasa (Joint National Association of Persons with Disabilities, JONAPWD), reshen Jihar Anambra, ya yi alƙawarin tattaro dukkan naƙasassu domin su shiga cikin wannan zaɓe.