Yayin da bai fi saura shekara ɗaya da rabi a yi zaɓen 2023 ba, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada hasashen cewa mai yiwuwa ne a yi wa sababbin jam’iyyun siyasa rajista kafin manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bada wannan hasken a wurin babban taron shekara-shekara na jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki wanda aka yi a Abuja.
Kalamin ya fito ne a cikin jawabin da wakilin sa a taron, Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Tuntuɓa a hukumar, Dakta Adekunle Ogunmola, ya gabatar a taron mai taken: “Jam’iyyun Siyasa da Ɗorewar Dimokiraɗiyya a Nijeriya: Nuna Alƙibla Ga Manyan Zaɓuɓɓukan 2023.”
Bugu da ƙari, kafin zaɓuɓɓukan na 2023, ahugaban hukumar ya bayyana damuwa kan yadda jam’iyyun siyasa su ke gudanar da harkokin su, ya ce ya kamata su yi gyara.
Ɗaya daga cikin matsalolin su da ya nuna su ne rashin bin tsarin dimokiraɗiyya a cikin jam’iyya, ninanci, ware mata da naƙasassu da kuma matasa.
A yayin da shugaban ke nuna yiwuwar yi wa ƙarin jam’iyyu rajista kafin lokacin manyan zaɓuɓɓukan, ya kuma bayyana cewa hukumar na sa ran cewa matsalolin da ke akwai a ƙasar nan ba za su zama barazana ga aiwatar da manyan zaɓuɓɓukan 2023 ba.
Ya ce, “Ina ganin cewa irin wannan babban taron ya na da muhimmanci a wajen yadda mu ka yi nazarin yanayin siyasar ƙasar nan ta hanyar yadda jam’iyyun ke taka rawar su, kuma mun gano wasu matsaloli da mu ke buƙatar a warware, kuma wannan shi ne dalilin shirya irin wannan taron, saboda abin da su ka samar a nan a yi amfani da shi wajen gyara tsarin siyasa.
“Don haka, babu wani abu a tsarin mu da ya ce kada mu ci gaba da yi wa jam’iyyun siyasa rajista in dai sun cika dukkan ƙa’idoji. Saboda haka dukkan ƙungiyoyin da ke so a yi masu rajista, a shirye INEC ta ke ta yi masu rajistar sai dai idan sun kasa cika ƙa’idojin.
“Yardar mu dai na ga Allah, mun taɓa samun irin wannan yanayin a baya kuma mun samu damar magance shi kuma mu na fatan a wannan karon, za a yi zaɓuɓɓukan 2023 cikin nasara fiye da zaɓuɓɓukan baya.”
A nasa ɓangaren, Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Tsare-tsare da Dabarun Mulki ta Nijeriya (NIPSS), Birgediya-Janar Chukwuemeka Udaya (ritaya), ya shawarci jam’iyyu da su gyara tsare-tsaren su wajen faɗaɗa tare da rungumar membobin su wajen tafiya tare da mata da matasa.
A yayin da ya ke nuna wasu daga cikin matsalolin yanayin siyasar ƙasar nan, Udaya ya ce jam’iyyu na buƙatar su gyara hanyoyin gudanarwar su don tabbatar da ƙarin taka rawar mata da matasa.
Ya ce, “Akwai mishkiloli da yawa irin su tsarin dimokiraɗiyyar cikin jam’iyyu, ninanci; buƙatar ƙarin taka rawar mata, buƙatar shigo da matasa; da buƙatar rungumar mutane masu fama da naƙasa (PWDs), ba kawai a matsayin masu jefa ƙuri’a ko membobin jam’iyya kaɗai ba har ma a matsayin shugabannin jam’iyyun siyasa da kuma a matsayin zaɓaɓɓun wakilan jam’iyyun siyasa.”
Udaya ya kuma shawarci ‘yan siyasa da kada su kalli lamarin siyasa a matsayin a mutu ko a yi rai.
Ya ce, “Abin da mu ke so jam’iyyu su ɗauka daga wannan taron ƙara wa juna sani shi ne kowane ɗan Nijeriya ya rage rarrabuwar kan da ke akwai; akwai manyan rarrabuwar kai kuma haƙƙin jam’iyyu ne su haɗe kan ƙasar nan, su ɗora ƙasar a kan alƙibla da turbar zaɓuɓɓukan 2023.
“Alƙiblar a bayyane ta ke, akwai al’amuran tsaro, akwai al’amuran tattalin arziki, kuma waɗannan su ne abubuwan da mu ke so su tattauna a kan su idan shekarar 2023 ta ƙarato.”
An shirya taron ne don a samar da alƙibla game da zaɓuɓɓukan 2023 kuma a wayar da kan jam’iyyu game da 2023.
Waɗanda su ka shirya taron su ne NIPSS, tare da haɗin gwiwar Tarayyar Turai (EU); Cibiyar Shugabannin Jam’iyyun Siyasa da Cigaban Tsare-tsare (Parties Leadership and Policy Development Centre) da sauran masu ruwa da tsaki.